Buhari: PDP za ta kwace mulki daga hannun APC idan har bata magance rikice-rikicenta ba

Buhari: PDP za ta kwace mulki daga hannun APC idan har bata magance rikice-rikicenta ba

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja kunne, inda yace matsawar jam’iyyarsa ta APC ba ta shirya rikicin cikin ta ba, PDP za ta amshi mulki a 2023
  • Buhari ya furta hakan ne yayin wata tattaunawa da NTA ta nuna shi a ranar Alhamis, inda yace shi kan shi sau uku ya tsaya takara sannan ya samu nasara, don haka duk mai son mulki sai ya dage
  • Ya ce a duba yadda PDP ta kasa ja da APC bayan jam’iyyu irin ACN, ANPP da CPC da sauransu sun dunkule wuri guda, take anan su ka ci galaba akan jam’iyyar

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ja kunne inda ya ce matsawar jam’iyyarsa, APC ba ta gyara duk wasu rigingimun da ke cikin ta ba, jam’iyyar adawa ta PDP za ta amshi mulki a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Buhari: Tsufa ya fara nuna wa a jiki na amma dai nagode wa Allah

Shugaban kasa Buhari ya furta hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi wanda NTA ta nuna ranar Alhamis da dare, Vanguard ta ruwaito.

Idan jam’iyyar APC ba ta magance rikicinta ba, PDP za ta amshi mulki, Buhari
Idan har jam'iyyar APC bata magance rikice-rikicenta ba, PDP za ta kwace mulki, Buhari. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Facebook

Shugaban kasan ya kara da cewa ya yi takarar shugaban kasa har sau uku kafin ya samu nasara, don haka duk wani mai son zama shugaban kasa sai ya yi aiki tukuru a kan kudirinsa, rahoton Vanguard.

Ya ce har yanzu akwai lokacin da za a gyara matsalolin cikin jam’iyyar

Bayan an tambaye shi akan ko jam’iyyar APC za ta iya gyara a kan matsalolin da ta ke fuskanta, cewa ya yi:

“Eh, mu na da lokaci. Sai mun yi aiki tukuru saboda kundin tsarin mulki ya bayar da shekaru 4 ne.

Kara karanta wannan

Ba za ku tsira ba: Buhari ya magantu kan masu koma wa APC don gujewa EFCC

“Babu wanda zai iya shiga. Don haka idan jam’iyyar ba ta kara dunkule kan ta wuri guda ba, jam’iyyar adawa za ta ci galaba a kan ta.”

Sai da jam’iyyu su ka yi maja sannan su ka ci galaba a kan PDP

Buhari ya kara da cewa:

“Me PDP ta yi? Sun kasa dunkulewa wuri guda. Amma lokacin da ACN, ANPP da CPC suka hade kai wuri guda su ka zama APC, kafin PDP ta farga, har an fatattake ta."

Ya kara da cewa har yanzu ba a maganar su (PDP). Su na ji su na gani.

Buhari: Tsufa ya fara nuna wa a jiki na amma dai nagode wa Allah

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana fatan ya kammala wa'adin mulkinsa lafiya domin 'tsufa ya fara kama shi', Daily Trust ta ruwaito.

Buhari, wanda ya cika shekaru 79 a ranar 17 ga watan Disamban 2021, ya bayyana hakan ne yayin amsa tambaya a tattaunawa da aka yi da shi a NTA, a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Gazawa: Buhari ya bayyana abin da yake ji a ransa idan aka ambaci PDP a kusa dashi

"Game da shekaru na, ina ganin sa'o'i na, yanzu suna hutawa ne, kuma ina tabbatar maka nima ina fatan ganin bayan watanni 17 nan gaba da zan samu in ɗan huta," in ji shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164