Takarar shugaban kasa a 2023: Kwankwaso ya magantu kan yiyuwar tsayawarsa takara
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya magantu a kan batun tsayawarsa takarar shugaban kasa a babban zaben 2023
- Kwankwaso ya ce har yanzu bai yanke shawara ba domin baya gaggawa, amma ya ce yana nan yana tuntubar mutanen da suka dace
- Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce suna da karfin da za su iya lashe kowani zabe saboda yawan tawagarsa a Najeriya da ma kasashen ketare
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewar har yanzu bai yanke shawara kan ko zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba.
Kwankwaso, a wata hira da DW Hausa a ranar Laraba, 5 ga watan Janairu, ya ce baya gaggawa don yin takara, inda ya kara da cewar yana kan tattaunawa da mutanen da suka dace.
An samu sauyi: Bayan ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda, Buhari ya bayyana yadda zai yake su
Kwankwaso ya ce:
"Yawanci a irin wannan bama gaggawa, sai an yi nazari, sai an taba mutanen da ya dace, mutanen da suke da hakki a kan al'amarin, kuma abun da aka samu aka fahimta, toh kuma sai a dauki mataki a kai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Kuma Allah ya kai mu wannan lokaci, idan Allah ya yarda za mu sanar da ku matsayin da Rabiu Kwankwaso zai dauka a kan abun da yake ya shafi zabe na 2023.
"Duk da cewar al'ummarmu tana nan gabas da yamma, kudu da arewa. Wasu sun dauka yan Kwankwasiyya ne kawai suke a Kano babu a wani wuri, wasu kuma sun dauka a ma a arewa maso yamma ne, wasu su ce arewa ce.
"Amma wadanda suka sani sun sani ba ma maganar Najeriya ake ba, Kwankwasiya tana nan musamman a kasashen Afrika, kasashen Asiya, Amurka, Turai ko'ina ka je akwai yan Kwankwasiyya, wurare da yawa ma muna da ofishoshi."
Ga bidiyon hirar tasu a kasa:
Kwankwaso ya fitar da magoya daga duhu kan batun barin PDP da neman Shugaban kasa
A halin da ake ciki, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana mai gamsarwa game da rade-radin da ake ji na cewa zai sauya sheka.
Kwankwaso yace babu gaskiya a jita-jitar da ke faman yawo a gari. Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya yi mulki sau biyu a jihar Kano, yace a halin yanzu bai yi wani zama da wasu a kan shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki ba.
A cewar Sanata Kwankwaso, ba yau aka saba yada irin wannan jita-jita ba, yace bini-bini a kan fito ana karyar yana shirin ficewa daga jam’iyyar hamayya ta PDP.
Asali: Legit.ng