Kaduna: Isa Ashiru, tsohon dan takarar PDP, ya bayyana niyarsa na sake fitowa takarar gwamna
- Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a 2019 karkashin jam’iyyar PDP, Hon Isa Kudan Ashiru, ya ce magudin zabe aka yi masa a shekarar 2019 amma ya ci nasara
- Ya bayyana kudirinsa na kara tsayawa takarar a shekarar 2023 kuma ya ce babu gudu babu ja da baya, zai jajirce har sai ya samu nasara
- Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai inda yace zai inganta tsaro da tattalin arzikin jihar, inda yace ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare
Kaduna - Dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP a shekarar 2019, Hon Isa Kudan Ashiru ya ce shi ya samu nasara a zaben 2019 amma magudi aka tafka masa, amma zai kara tsayawa takarar a shekarar 2023, Vanguard ta ruwaito.
Ya kara da cewa yana siyasa ne don yi wa mutane aiki sannan ya shayar da jama’ansa romon dimokradiyya.
Ita ma The Cable ta rahoto cewa Dan siyasar ya bayyana kudirinsa yayin tattaunawa da manema labarai a Kaduna inda ya ce zai kara tsayawa takarar a karkashin jam’iyyar PDP kuma a cewarsa babu gudu babu ja da baya.
Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare
Kamar yadda dan takarar ya ce:
“Ina da burin jajircewa a kan wannan kudirin nawa har sai na samu nasara.”
Idan ba a manta ba Ashiru ya rike kujerar dan majalisar tarayyar jihar Kaduna har sau biyu sannan ya dare kujerar dan majalisar wakilai shima har sau biyu.
Ya tsaya takara tare da Gwamna Nasir El-Rufai a karkashin jam’iyyar APC a 2015 sai dai tun a zaben fitar da gwani ya sha kaye wanda daga nan ya koma jam’iyyar PDP kafin zaben 2019.
A 2019 ya tsaya takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP amma El-Rufai ya kayar da shi. Sai dai ya tsaya akan cewa magudin zabe aka yi masa don bai yarda ya fadi ba, sannan ya yi alkawarin kara tsayawa takara a 2023.
Ashiru ya ce yana da burin inganta tsaro a jihar Kaduna
Kamar yadda Ashiru ya kada baki yace:
“Abu ne mai burgewa. Idan ka sha kaye a siyasa, ba faduwa kayi ba. Wannan wasan ba akai na ko mutane na bane. Ina da buri wanda nake tunanin idan na samu dama zan sauya rayuwar mutane da dama kuma ta inganta.
“Don haka ban shigo siyasa ba sai don in gyara halin da mutane su ke ciki na tabarbarewar tattalin arziki da kuma yanayin rayuwa, hakan ya sa na dage ina neman kujerar.”
Ya kara da cewa yana da burin ganin ya yi mulki mai kyau don samar da isasshen tsaro a fadin jihar kuma ya yi shugabanci cike da tsoron Ubangijinsa.
Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa
A wani labarin, Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanar da korar surukinsa, Mataimakin Manajan, Hukumar Kare Muhalli ta JIhar Abia, ASEPA, ta Aba, Rowland Nwakanma, a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.
A cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barista Chris Ezem ya fitar, Ikpeazu ya kuma 'sallami dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli a Aba amma banda na Aba-Owerri Road, Ikot Ekpene da Express.'
Amma gwamnan ya bada umurnin cewa dukkan 'masu shara ba a kore su ba, su cigaba da aikinsu na tsaftacce hanyoyi da tituna a kowanne rana.
Asali: Legit.ng