Masu suka ba za su gane Buhari rahama ne ga 'yan Najeriya ba har sai ya sauka – Minista
- Karamin ministan ayyuka da gine-gine, Mu'azu Sambo, ya bayyana Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin rahama ga 'yan Najeriya
- Sai dai ya ce masu suka ba za su gane hakan ba sai bayan ya sauka daga kan mulki
- Sambo ya kuma ce hanyar da shugaban kasar ya dauka domin bunkasa ababen more rayuwa a kasar ita ce daidai
Sabon karamin ministan ayyuka da gine-gine, Mu'azu Sambo, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki hanyar da ta dace domin bunkasa ababen more rayuwa a kasar.
Ya bayyana hakan yayin da ya kama aiki a ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, sannan ya samu tarba daga sakataren din-din-din, Babangida Hussaini, da ma'aikatan ma'aikatar.
Sambo ya tabbatar da cewa ’yan Najeriya, wadanda ke shakka a kan iyawar Buhari za su gane muhimmancinsa ne bayan gwamnatinsa ta kare, jaridar Punch ta rahoto.
Sambo ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Shugaban kasa alkhairi ne ga kasar nan. Ina kara fada cewa masu shakku ba za su gane hakan ba har zai shugaban kasar ya tafi. Amma wasunmu da suka san cewa ci gaban zamantakewa da tattalin arziki yana da nasaba da dimbin ayyukan samar da ababen more rayuwa, mun san cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi hanyar da ta dace."
Ya bayyana cewa, samar da ababen more rayuwa na da muhimmanci ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kowace kasa.
Hakazalika ya yi misalai da kasashen Sin da Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa a matsayin kasashe masu gasa saboda zuba jarin da suka yi na samar da ababen more rayuwa.
Ya bayyana cewa zai cimma hakan a tsakanin lokacin da zai kasance a ma'aikatar don taimakawa shugaban kasar wajen barin wasu tarihi a bangaren ci gaban more rayuwa a fadin kasar.
Ya bayyana cewa a shirye yake ya yi aiki tare da babban ubangidansa, Babatunde Fashola, wanda ya bayyana a matsayin mutum mai hazaka, gwaninta kuma mai kishin ci gaba, rahoton Thisday.
Majalisar dattawa ta amince da naɗin sabon Minista, Muazu Sambo
A baya mun kawo cewa majalisar dattawan tarayyan Najeriya ta tabbatar da Mu'azu Sambo, a matsayin sabon minista Lantarkia Najeriya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Babbar majalisar ta amince da naɗinsa ne bayan kwashe fiye awa ɗaya tana tantance shi ranar Talata 21 ga watan Disamba.
Ana tsammanin za'a rantsar da Sambo a matsayin sabon minista biyo bayan tabbatar da shi da majalisar dattawa ta yi.
Asali: Legit.ng