'Yan Najeriya Na Alfahari Da Buhari, In Ji Kakakin Majalisar Wakilai, Gbajabiamila
- Femi Gbajabiamila, Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya ya mika sakon fatan alheri ga Shugaba Buhari yayin da ya cika shekaru 79
- Gbajabiamila, cikin sakon da ya fitar da hanun hadiminsa Lanre Lasisi ya ce 'yan Najeriya suna alfahari da Shugaba Muhammadu Buhari
- Kakakin Majalisar ya ce 'yan kasar na alfahari da yadda Shugaba Buhari ya rika jagorancin kasar tun zabensa karo na farko a shekarar 2015
Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayyar Najeriya, Femi Gbajabiamila, a ranar Alhamis 'ya ce 'yan Najeriya suna alfahari da Shugaban Kasa Muhammdu Buhari, Tribune ta ruwaito.
Ya ce suna alfahari da yadda shugaban kasar ya rika jan akalar mulkin kasar tun lokacin da aka fara zabensa a karo na farko a shekarar 2015.
A cikin sanarar da hadiminsa a bangaren watsa labarai, Lanre Lasisi ya fitar domin taya Shugaban kasar murnar cika shekara 79 da haihuwa, Kakakin Majalisar ya ce Buhari ya yi wa 'yan Najeriya abubuwan alheri.
Gbajabiamila ya ce kamata a ranar zagayowar haihuwarsa, 'yan Najeriya su rika karrama mutum irin Buhari wanda a duk abin da ya ke yi kasa ya ke saka wa a gaba, The Nation ta ruwaito.
Kakakin ya ce:
"Shugaban Kasa, Najeriya da 'Yan Najeriya suna alfahari da kai. Abin yabo ne da jinjina yadda ka rika tafiyar da harkokin mulkin Najeriya.
"Don haka, na shiga sahun miliyoyin masu kishin kasa don taya ka murnar zagayowar ranar haihuwar ka kuma muna maka fatan alheri da karin shekaru cikin koshin lafiya."
Wasu jiga-jigai a arewa sun so su hana APC tsayar da Buhari takara a 2015, Bisi Akande
A wani labarin, Bisi Akande, tsohon shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya ya ce akwai wasu shugabannin arewa da su ka nemi kada jam’iyyar ta tsayar da Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takara a 2015, The Cable ta ruwaito.
A littafin tarihin rayuwarsa na “My Participation”, Akande ya ce akwai wasu sanannun shugabannin gargajiya da su ka so a hana tsayar da Buhari a matsayin dan takara don gudun janyo wa arewa matsaloli.
Marubucin ya kara da cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya nemi shugabannin jam’iyyar APC kada su kuskura su tsayar da Buhari a matsayin dan takara.
Asali: Legit.ng