Boye N19bn: Gwamnatin Kogi ta kai EFCC kotu, ta bukaci a biya ta N35bn na 'bata suna'

Boye N19bn: Gwamnatin Kogi ta kai EFCC kotu, ta bukaci a biya ta N35bn na 'bata suna'

  • Gwamnatin jihar Kogi ta je kotu a kan zargin EFCC na cewa ta boye wasu Naira biliyan 19.3 a banki
  • Babban akawun jihar Kogi da wani kwamishina suka kai karar hukumar EFCC a wani kotu a jihar
  • Lauyoyin jihar Kogi suna so Alkali ya tursasawa EFCC ta biya su N35bn saboda bata masu suna

Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta shigar da karar EFCC a gaban kotu a kan zargin da tayi mata na cewa ta boye N19.3bn da ta karba daga gwamnatin tarayya.

Jaridar The Cable tace babban akawun jihar Kogi, Momoh Jibrin, da kwamishinan kudi da tattali, Asiwaju Mukadam Asiru, sun kai kara a babban kotun jihar.

Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya da wani banki da CBN ne wadanda za su kare kansu a wannan shari’a da ta ke gaban Alkali mai shari’a J. Majebi.

Kara karanta wannan

Yadda wani gwamna a Arewa ya kwashi tsabar kudi biliyan N60bn daga lalitar jiharsa, EFCC ta magantu

Alkali ya fadawa EFCC ta yi hattara

Mai shari’a J. Majebi na babban kotun jihar Kogi, ya bada umarni ga EFCC ta daina wallafa wani bayani a game da wannan magana da yanzu ta na gaban kotu.

Alkali ya ja-kunnen EFCC a kan yin magana game da abin da ya shafi wannan banki da asusu mai lamba 0073572696 wanda gwamnatin jihar Kogi ta mallaka.

Gwamnatin Kogi
Yahaya Bello da Buhari BBCNewsHausa
Asali: Facebook

Gwamnatin jihar ta na bukatar a biya ta Naira biliyan 35 saboda bata mata suna da tace hukumar ta EFCC ta yi a dalilin wani rahoto da ta fitar a Nuwamban 2021.

Vanguard tace EFCC tayi wa wannan rahoto da ta fitar a shafinta na Facebook kwanaki take da ‘Hidden N19.3 billion Kogi salary bailout funds returned to CBN’.

Kara karanta wannan

Karbe wayar Sowore ta jawowa Jami’an DSS matsala a kotu, Alkali yace su biya shi N2m

Gwamnatin Kogi ta karyata zargin da ake yi mata na boye kudi a banki, ta ce har yanzu abin take da shi a asusu bai kai N20bn, duk da zargin an boye biliyoyin.

Ba a nan kawai EFCC ta tsaya ba

Bugu da kari, gwamnatin Kogi ta roki kotu ta tursasawa EFCC ta yadda za ta fitar da sakon neman afuwa nan da kwanaki biyu domin ta bada hakuri a gidajen jaridu.

Lauyoyin jihar ta Kogi su na so hukumar EFCC ta bada hakuri a kan irin rubuce-rubucen da ta rika yi, wanda a cewar gwamnatin jihar, soki-burutsu ne ba komai ba.

A ranar 17 ga watan Disamba, 2021, za a saurari wannan kara kamar yadda kotu ta bayyana.

A watan da ya wuce hukumar EFCC ta sanar da cewa ta maidawa babban bankin Najeriya da kudi har N19.3 biliyan da ta samu an boye a asusun gwamnatin jihar Kogi.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutumin da aka kama da ATM 2,863 a Legas

Maida kudin kusan biyayya ne ga hukuncin wata babbar kotun tarayya da ke Ikoyi a jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel