Yari Vs Matawalle: Kotu ta yanke hukunci kan rikicin jam'iyyar APC a Zamfara

Yari Vs Matawalle: Kotu ta yanke hukunci kan rikicin jam'iyyar APC a Zamfara

  • Kotun tarayya ta yi watsi da karar da jam'iyyar APC na tsagin Abdul-aziz Yari ta shigar kan shugabannin APC a Zamfara
  • A cewar alkalin, Mai sharia Aminu Bappa, kotu ba ta da hurumin shiga harkokin wata jam'iyyar siyasa na cikin gida
  • Wasu tsofaffin shugabannin kananan hukumomi 10 dake goyon bayan Yari ne suka shigar da kara gaban kotu

Zamfara - Babbar kotun tarayya dake zamanta a Gusau, ta yi fatali da karar da tsofaffin ciyamomin APC 10 dake goyon bayan tsohon gwamna, Abdul'azizi Yari suka shigar gabanta.

Channels tv ta rahoto cewa wani Abdul-aziz Danmaliki da wasu mutum 9 ne suka shigar da karar a watan Yuli, suna kalubalantar matakin APC ta ƙasa.

Masu shigar da karar sun kalubalanci matakin kwamitin rikon kwarya na APC karkashin gwamna Mai Mala Buni, na rushe shugabannin APC a Zamfara bayan sauya shekar gwamna Matawalle.

Kara karanta wannan

Farfesa Jega ya fallasa dabarun Alkalai, ya bayyana yadda suke samun kudin haram

Yari Vs Matawalle
Yari Vs Matawalle: Kotu ta yanke hukunci kan rikicin jam'iyyar APC a Zamfara Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da yake yanke hukunci ranar Jumu'a, Mai sharia Aminu Bappa, ya bayyana cewa kotun tarayya ba ta da hurimin shiga harkokin wata jam'iyyar siyasa.

Ya ƙara da cewa lamarin yana da alaƙa da wata matsala ta cikin gida, wanda kotu ba ta da ikon yin katsalandan ta tsoma baki a ciki.

Gwamna Mai Mala Buni, shine na farko da masu shigar da kara suka maka a kotu, sai kuma jam'iyyar APC ta biyu, da hukumar zaɓe a matsayin ta uku.

Abinda yasa suka shigar da ƙara

A jawabinsa, shugaban tawagar masu shigar da kara, Daniel Enwelum, ya roki kotu ta duba ko matakin da kwamitin Mala Buni ya ɗauka na rushe shugabannin APC a jihar, tare da mika ragamar komai hannun gwamna Matawalle na kan doka.

Kara karanta wannan

Hotunan Gwamnonin PDP sun tafi filin kwallon Real Madrid a Kasar Spain

A korafin da suka shigar, masu kara sun bukaci kotu ta yi watsi da matakin rushe APC a Zamfara kuma ta umarci INEC kada ta amince da wasu shugabanni in ba na tsagin su ba.

Hakanan kuma sun bukaci kotu ta hana Mala Buni da APC dakatar da wa'adin su a Ofis, wanda zai kare lokacin da aka kammala zaɓen sabbin shugabanni a kowane mataki.

Wane mataki zasu ɗauka a gaba?

Amma da yake martani kan hukuncin kotun, Enwelum (SAN), yace zasu yi nazari kan matakin da kotu ta ɗauka kafin su san abinda zasu yi nan gaba.

Tribune Online Lauyan yace:

"Masu shigar da ƙara zasu yi nazari kan hukuncin kotun, idan sun gamsu shikenan. Idan kuma suna da ja, zasu iya ɗaukaka kara zuwa gaba."

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta ƙasa ta bayyana matakin da zata dauka kan Ganduje da Shekarau bayan hukuncin Kotu

Kara karanta wannan

Ba zata saɓu ba, Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan Kwamishina a jihar Katsina

Jam'iyyar APC tace har yanzun tana dakon kwafi na asali na hukuncin da kotu ta yanke kan zaɓen shugabanni a Kano.

Sakataren APC na kasa, Sanata James, yace jam'iyya zatai nazari kan hukuncin kafin ta ɗauki matakin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262