Jam'iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi 16 da kansiloli a jihar Ekiti
- Jam'iyyar APC ta samu nasara a baki ɗaya kujerun da aka fafata a zaben kananan hukumomin jihar Ekiti.
- Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta, Jide Aladejana, yace APC ta lashe kujerun ciyamomi 35 da kansiloli 176 cikin 177
- Sai dai babban jam'iyyar hamayya, PDP, bata shiga zaben ba, kuma ta yi ikiratin cewa APC ba zata iya shirya sahihin zaɓe ba
Ekiti - Jam'iyyar APC mai mulki ta lashe baki ɗaya kujerun ciyamomi 35 da kansiloli 176 cikin 177 a zaben kananan hukumomi da ya gudana a jihar Ekiti ranar Asabar.
Tribune Online ta tattaro cewa zaben ya gudana a dukkan kananan hukumomi 16 da kuma yankuna 19, da gundumomi 177 dake faɗin jihar.
Babbar jam'iyyar hamayya PDP bata shiga zaɓen ba, ta kuma yi ikirarin cewa APC ba zata shirya sahihin zaɓe ba a jihar.
Jam'iyyun siyasa shida da suka fafata a zaɓen sun haɗa da jam'iyyar AA, jam'iyyar ADC, APGA, NRM, YPP da kuma jam'iyyar APC.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya sakamakon zaɓen ya kasance?
Da yake bayyana sakamakon zaɓen ranar Lahadi, shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar, Justice Jide Aladejana, yace APC ta lashe ƙujerun kansiloli 176 cikin 177 dake faɗin jihar.
Aladejana yace an dage zaɓen gundumar Erinjiyan sabida rikicin da ya ɓarke a garin yayin da ake gudanar da zaɓe.
Ya yaba wa hukumomin tsaro, ma'aikatan hukumar zaɓe, da kuma masu kaɗa kuri'a bisa haɗin kan da suka bayar wajen tabbatar da zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali.
PDP ta yi martani
Sai dai a nata bangaren, jam'iyyar PDP reshen jihar Ekiti, ta yi watsi da zaɓen wanda aka bayyana APC ta samu nasara a kowace kujera.
Kakakin PDP na jihar, Raphael Adeyanju , shine ya bayyana haka a wata sanar da aka raba wa manema labarai a Ado-Ekiti.
Punch ta rahoto Yace:
"Maganar gaskiya yanzun a Najeriya APC ba zata iya kai bantenta a kowane irin zaɓe aka fafata ba kuma a kowace jiha."
"Kasancewan babu wata jam'iyya daga cikin sauran jam'iyyu da ta ci kujerar kansila ɗaya, ya nuna rashin adalcin APC."
A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar APC ta yi magana kan shirin gwamna Umahi na sauya sheka zuwa PDP
Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Ebonyi, ta musanta jita-jitar cewa gwamna Dave Umahi na shirin sauya sheƙa zuwa PDP.
Kakakin APC na jihar, Simbard Ogbuatu, ya roki mambobin da sauran al'umma su yi watsi da labarin domin ba shi da tushe.
Asali: Legit.ng