Jam'iyyar APC ta yi magana kan shirin gwamna Umahi na sauya sheka zuwa PDP

Jam'iyyar APC ta yi magana kan shirin gwamna Umahi na sauya sheka zuwa PDP

  • Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Ebonyi, ta musanta jita-jitar cewa gwamna Dave Umahi na shirin sauya sheƙa zuwa PDP
  • Kakakin APC na jihar, Simbard Ogbuatu, ya roki mambobin da sauran al'umma su yi watsi da labarin domin ba shi da tushe
  • Yace Umahi ya shiga APC ne domin kawo cigaba a jihar Ebonyi da kudu maso gabashin Najeriya baki ɗaya

Ebonyi - Jam'iyyar APC mai mulki reshen jihar Ebonyi, ta bayyana cewa jita-jitar cewa gwamna Dave Umahi na shirin komawa PDP ƙanzon kurege ne.

Kakakin APC reshen jihar, Simbard Ogbuatu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a a Abakaliki.

Daily Nigerian ta rahoto kakakin APC na yin kira ga mambobin jam'iyyarsu kan su yi watsi da raɗe-raɗin wanda ba shi da tushe.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa muka nemi yan sanda sun cafke hadimin Danjuma Goje, Jam'iyyar APC ta magantu

Gwamna Umahi
Jam'iyyar APC ta yi magana kan shirin gwamna Umahi na sauya sheka zuwa PDP Hoto: dailpost.ng
Asali: UGC

Ogbuatu yace:

"APC a Ebonyi ta samu labarin ana yaɗa wata jita-jita a kafafen sada zumunta mai taken, 'Orji Kalu, Dave Umahi sun ƙagu su koma jam'iyyar PDP' kuma aka jingina wa jigon PDP a Abia, Dakta Isaac Nkole."
"Rahoton ya nuna Dakta Nkole na cewa Gwamna Dave Umahi na son komawa jam'iyyar PDP."
"Amma muna mai bayyana cewa Gwamna Umahi bai taba shirin komawa cikin PDP ba, ko dakansa, ko ya aika wakilai, gwamnan mu be yi wani shirin komawa wannan tawagar yan Club ɗin ba."

Umahi ne jagoran APC a Ebonyi

Mista Ogbuatu ya kara da cewa gwamnan Umahi ya kwashe sama da shekara ɗaya yana jagorantar APC a Ebonyi kuma jam'iyyar ta zama tamkar gidansa.

A cewarsa, Umahi bai sauya sheka zuwa APC mai mulki domin bukatarsa ba, amma sai don cigaban jihar Ebonyi da yankin kudu maso gabas baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Jigon PDP ya bayyana sunayen gwamnan APC da tsohon gwamna dake shirin sauya sheka zuwa PDP

Ogbuatu yace gwamnan ya koma APC ne domin haɗa karfi da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da sauran masu kishin ƙasa wajen ɗaga Najeriya zuwa mataki na gaba.

Ya tabbatar da cewa a mulkin shugaban kasa Buhari, babu wani ɓangaren yankin kudu maso gabas da bai amfana da ayyukan cigaba na more rayuwa ba.

A wani labarin kuma tsohon gwamna, Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan rikicin Ganduje da Shekarau a APC jihar Kano

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace rikicin da ya baibaye jam'iyyar APC reshen Kano bai zo masa da mamaki ba.

Kwankwaso ya ɗora laifin akan gwamnan Kano na yanzu, Dakta Abdullahi Ganduje, inda yace halinsa na son kai ya jawo wannan rikicin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262