Gwamnan Benue: Ubangiji ne ya zo min yace na sake tsayawa takarar gwamna
- Gwamnan jihar Benue ya bayyana yadda ubangijinsa ya zabe shi don sake tsayawa takara a zaben 2019
- Ya shaidawa 'yan jiharsa cewa, shi ba da son ransa ya sake tsayawa takarar gwamna a jihar ta Benue ba a 2019
- Ya kuma ce, bai kamata 'yan jihar suke zaginsa da cin mutuncinsa ba kasancewarsa zababbe daga ubangijinsa
Benue - Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Samuel Ortom ya ce bai so tsayawa takara a zaben 2019 saboda zagin da yake sha daga 'yan adawar sa.
Ortom, wanda aka sake zaba shekaru biyu da suka wuce, ya bayyana hakan a lokacin da ya kaddamar da babban cocin Pentecostal, wani sabon ginin ofishin jakadancin Christian Network a Makurdi, babban birnin jihar.
'Dan sanda ya gano matarsa na faɗa wa samarinta bata da aure, ya faɗa wa kotu shima ya haƙura da ita
Ya ce sai da yayi azumin wata uku, inda ya ce ubangiji ya ba shi umarnin sake tsayawa takarar gwamna.
A cewarsa:
“A shekarar 2017, na yanke shawarar cewa ba zan sake tsayawa takara karo na biyu ba kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya amince da shi kuma saboda cin mutuncin da ‘yan Benue suka yi min da kuma yadda aka rika zagi na.
“Hatta wasu ’yan coci sun hada baki da wadanda ba su san Allah ba, na ji zafi a zuciyata na ce ‘ubangiji kai ka kawo ni’ na ce ba zan tsaya takara a zaben 2019 ba.
“A daren nan, ubangiji ya tsawata mini, ya gaya mani. ‘Ban gama da kai ba. Ni na kawo ka, ban ki ka ba, lokacin da mutane suka ki ka, har yanzu ina tare da kai.
“Na yi azumi na wata uku, na yi nazarin rayuwar Annabi Musa a cikin littafin Exodus na cikin Littafi Mai Tsarki kuma a karshe, ubangiji ya ce mini, kada ka zama kamar Musa wanda bai iya cimma Kasar Alkawari ba, ka yi imani da ni, ni kuma zan tsaya maka har karshe."
Ortom ya gargadi wadanda suka sadaukar da lokacinsu wajen bata shi da su yi hattara domin shi zababbe ne daga ubangijinsa.
Ya ce ko da ya yi kuskure, ya kamata mutane su yi masa addu’a, kada su zarge shi da zalunci, kamar yadda tashar yanar gizo ta Reuben Abati ya tattaro.
Ya kara da cewa:
“Bana son ku (mutanen Benue) ku fuskanci fushi da hukuncin ubangiji ta hanyar zagin wanda ubangiji ya zaba. Ko da ina yin abin da bai dace ba, dole ne ku yi mini addu'a. Ba wai a raina ni da cin mutuncina da hada kai a ce Ortom yana sayen dukkan wasu kadarori na kasa ba."
Gwamna Ortom dan bindiga ne, 'yan bangan mu za su kama shi, Miyetti Allah
A wani labarin, kungiyar fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta kira gwamna Samuel Ortom na jihar Benue da dan ta’adda, kuma ta lashi takobin kama shi matsawar EFCC ba ta damke shi ba.
Kungiyar ta yi wannan furucin ne bayan gwamnonin kudu sun hana kiwon shanu a fili, dokar da suke dab da kafawa.
Miyetti Allah ta zargi gwamna Ortom kwarai inda ta ce dan ta’adda ne shi. Ta kuma bayyana wannan zargin ne ta sakataren ta na kasa, Saleh Alhassan, ya yin tattauna wa da gidan jaridar Leadership.
Asali: Legit.ng