Gwamna Ortom Ɗan Bindiga Ne, 'Yan Bangan Mu Za Su Kama Shi, Miyetti Allah
- Kungiyar fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta zargi gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom da ta’addanci
- Kungiyar ta lashi takobin cewa matsawar EFCC ba ta kama shi ba, ‘yan sintirin ta za su damke shi idan ya sauka daga mulki
- Kungiyar ta zargi gwamnan da fada da kungiyar Fulanin da kuma wawusar dukiyar jihar Binuwai
Makurdi, Benue - Kungiyar fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta kira gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai da dan ta’adda, kuma ta lashi takobin kama shi matsawar EFCC ba ta damke shi ba.
Kungiyar ta yi wannan furucin ne bayan gwamnonin kudu sun hana kiwon shanu a fili, dokar da suke dab da kafawa.
Miyetti Allah ta zargi gwamna Ortom kwarai inda ta ce dan ta’adda ne shi. Ta kuma bayyana wannan zargin ne ta sakataren ta na kasa, Saleh Alhassan, ya yin tattauna wa da gidan jaridar Leadership.
Miyetti Allah ta lashi takobin sanya ‘yan sintirin ta su kama gwamnan bayan ya sauka daga kujerarsa.
Sannan Alhassan ya zargi gwamnan da fada da kungiyar fulanin.
Dakatar da kiwo a fili zalunci ne kuma ba za mu taba amincewa da hakan ba,” a cewarsa.
Idan kana neman gawurtaccen dan ta’adda, ka nemi gwamna Ortom na jihar Binuwai. Don shi ne asalin dan ta’adda.
Alhassan ya zargi gwamnan da satar dukiyar jihar Binuwai. Ya kuma bayyana cewa matsawar EFCC ba ta kama shi ba, ‘yan Sintirin Miyetti Allah za su kama shi.
Kamar yadda yace,:
Jiran shi muke yi ya sauka daga mulki, matsawar EFCC ba ta damke shi ba, ‘yan sintirinmu za su damke shi.
Musulunci Ya Haramta: Ban Goyon Bayan Halasta Amfani Da Wiwi, Ƴan Majalisar Kano Ma Basu Goyon Baya, Ganduje
Rikicin Jos: Wasu Migayu Ne Ke Amfani Da Addini Da Siyasa Don Ganin Ba a Zauna Lafiya Ba a Plateau, Lalong
A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano, a ranar Litinin ya nuna rashin jin dadinsa kan yunkurin da ake yi na hallasta amfani da ganyen wiwi a Nigeria, The Nation ta ruwaito.
Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa, NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (mai murabus) da manyan jami'an hukumar suka kai masa ziyarar ban girma a Kano.
A sanarwar da kakakin NDLEA, Mr Femi Babafemi ya fitar, ya ce gwamnan ya ce babu wani dan majalisar tarayya daga jiharsa da zai goyi bayan irin wannan yunkurin, LIB ta ruwaito.
Asali: Legit.ng