Tsohon gwamna ga PDP: Ku bar tikitin shugaban kasa a zaben 2023 ga mai rabo
- Mu’azu Babangida Aliyu, tsohon gwamnan jihar Neja, ya shawarci jam'iyyar PDP da ta bar tikitinta na shugaban kasa a zaben 2023 ga mai rabo
- Aliyu ya ce maimakon bin tsarin karba-karba, kamata yayi jam'iyyar ta baiwa duk wanda ke ganin ya cancanta damar fitowa ya baje kwanjinsa
- Ya kuma bayyana cewa babbar jam'iyyar adawar kasar ta gane kura-kuranta a yanzu
Jihar Neja - Tsohon gwamnan jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu, ya bayyana cewa maimakon mika tikitin shugaban kasa na 2023 ga wani yanki, kamata yayi a bude shi ga yan Najeriya da suka cancanta.
Ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a wani shirin Daily Politics na Trust TV a ranar Laraba, 24 ga watan Nuwamba.
Aliyu ya tuna cewa ya kasance mamba a kwamitin shiya na jam'iyyar PDP wanda yayi rabon kujeru a baya.
Jaridar Daily Trust ta nakalto tsohon gwamnan yana cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Mun yanke shawara a wancan lokacin cewa misali, idan wani daga jihohin arewa ya zama shugaban kasa, toh ciyaman zai yi murabus sannan sai mu sake aiki. Muna da wannan tsarin a rubuce, mun sanya hannu a kai. Na yarda cewa za mu dawo kai idan lokacin yayi.
"Jam'iyyar bata dauki kowani matsayi ba a yanzu haka. Idan muka yarda kan cewa ya zama dole mulkin karba-karba yayi aiki, na tabbata za mu kafa wani kwamiti da zai yi aiki a kai. Sai dai, muna da rubutaccen matsaya cewa mu bar tikitin shugaban kasa a bude ta yadda duk wanda ke ganin zai iya takara zai samu damar fitowa tseren."
Ya kuma yi bayanin dalilin da yasa PDP ta fadi zabukan shugaban kasa a 2015 da 2019.
Aliyu ya ce:
"Abun da ya faru a 2015 da muka fadi zabe ya kasance rikicin cikin gida ne. a 2019, 'yan Najeriya da dama da ke iya kallon lamura da idon basira za su fada maka cewa PDP ta lashe zabe. Abu daya shine cewa ba mu ne ke jan ragamar abubuwar kasar ba."
Sai dai kuma, tsohon gwamnan ya ce PDP ta koyi darasinta. Ya ce jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ta bayar da gafarar sa ba kaho maimakon aiwatar da ainahin mulkin.
Kan zaben fidda gwani na wakilai majalisar dokokin kasar ta amince da shi a baya-bayan nan, ya ce ya kamata a gwada shi a zaben 2023.
2023: Saraki ya ziyarci wata jihar arewa kan kudirinsa na son hayewa kujerar Buhari
A wani labarin, mun kawo a baya cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya ziyarci Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue a ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba, kan kudirinsa na takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.
Saraki wanda yayi ganawar sirri da Ortom ya kuma gana da kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP a jihar domin sanar da su kudirinsa na fara tuntuba game da aniyarsa na shugabantar kasar, rahoton Daily Trust.
Ya bayyana cewa sauya shekar da masu biyayya ya jam’iyyar All Progessives Congress (APC) ke yi zuwa PDP a fadin kasar alamu ne da ke nuna cewa jam’iyyar na iya zama babu kowa kafin zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng