APC ta ba Buhari wuka da nama na tsayar da lokacin gudanar taron gangami
- Jam’iyyar APC ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai iya sanya ranar gudanar da taron gangamin APC na kasa da ake jira
- Ta bayyana hakan ne bayan da gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar suka yi taro a ranar Lahadi, 21 ga watan Nuwamba
- Shugaban PGF, Gwamna Abubakar Bagudu ya ce ranar da za a gudanar da taron gangamin na kasa ya wuce shawarin gwamnoni
Abuja – Gwamnonin jam’iyyar APC sun nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai tantance lokacin da taron gangamin jam’iyyar zai gudana.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa gwamnonin karkashin kungiyar Progressive Governors’ Forum (PGF) sun bayyana hakan a daren Lahadi, 21 ga watan Nuwamba a Abuja bayan sun gudanar da wani muhimmin taro na bayan fage.
Kusan gwamnonin APC 20 ne suka halarci taron wanda aka gudanar a dakin taro na gidan Gwamnonin Jihar Kebbi da ke Asokoro Abuja da misalin karfe 9:20 na dare.
Gwamna Abubakar Bagudu, shugaban kungiyar ya lura cewa kungiyar za ta nemi ganawa da Buhari domin tattauna batun taron gangamin da za a yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shirun da kwamitin tsare-tsare na rikon kwarya/CECPC da karkashin jagorancin Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya yi ya sa wasu ‘ya’yan jam’iyyar su ka yi tunanin matsala a jam'iyyar.
Sakataren kwamitin riko, Sanata John James Akpanudoedehe, ya ce masu ruwa da tsaki, ba kwamitin ba ne za su tsayar da ranar da za a gudanar da taron gangamin na kasa.
Wata majiya a taron Gwamnonin ta shaida wa jaridar The Nation cewa:
“Taron ya tattauna kan taron gangami na kasa amma an amince da ba wa shugaban kasa wuka da nama na sanya ranar da za a gudanar da taron."
Gwamnonin APC sun shiga ganawar sirri a Abuja
A baya kun ji cewa, Gwamnanonin jihohin Najeriya dake jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun shiga ganawar sirri a gidan ajiya bakin Gwamnan jihar Kebbi dake Abuja, ranar Lahadi, 21 ga Nuwamba 2021.
Daily Trust ta ruwaito cewa majiyoyi sun ce zaman bai rasa nasaba da lamarin taron gangamin jam'iyyar da ake shirin yi.
Wadanda ke hallare a tarin sun hada da Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule; da Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq.
Asali: Legit.ng