Rikicin APC: Jam'iyyar mu ba zata tarwatse ba, Gwamnonin APC sun magantu bayan saka labule

Rikicin APC: Jam'iyyar mu ba zata tarwatse ba, Gwamnonin APC sun magantu bayan saka labule

  • Gwamnonin APC mai mulki sun gana da juna a babban birnin tarayya Abuja domin tattauna abubuwa da dama da suka shafi jam'iyya
  • Gwamnonin sun amince za su garzaya gaban shugaban kasa, Muhammadu Buhari, domin shaida masa inda suka kwana
  • A cewarsu, jam'iyyar APC zata baiwa mara da kunya, kuma ba zata tarwatse ba kamar yadda wasu ke yaɗa wa

Abuja - Gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki a ranar Lahadi da daddare, sun gana da juna domin tattauna wa kan hanyoyin shawo kan matsalolin dake faruwa.

Vanguard ta rahoto cewa gwamnonin sun gudanar da wannnan taron ne musamman kan shirin gangamin taron APC na ƙasa, a cewarsu duk da rikicin dake faruwa APC ba zata tarwatse ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci Orji Kalu a Abuja

Taron wanda aka fara da misalin karfe 8:00 na dare cikin sirri, ya gudana ne a gidan gwamnan jihar Kebbi dake Asokoro, Abuja.

Gwamnonin APC
Rikicin APC: Jam'iyyar mu ba zata tarwatse ba, Gwamnonin APC sun magantu baya saka labule Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Akalla gwamnonin 20 ne suka samu halartan taron, cikinsu harda shugaban kungiyarsu, kuma gwamnan Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.

Sauran da suka halarci ganawar sun haɗa da gwamnonin jihohin Kogi, Nasarawa, Katsina, Plateau, Ekiti, Jigawa, Kano, Kwara, Imo, Borno, Ebonyi, Lagos, Zamfara, Niger, Ogun da Cross River.

Wane mataki gwamnonin suka ɗauka?

Gwamnonin sun cimma matsayar ganawa da shugaba Buhari kan garambawul ɗin da akai wa dokokin zabe, wanda majalisun tarayya suka amince da shi, musamman zaben fidda gwani kai tsaye.

Da yake zantawa da manema labarai bayan fitowa daga taron, shugaban gwamnonin, Atiku Bagudu, ya yi gum da bakinsa kan tsarin rarraba mukaman jam'iyya a matakin ƙasa.

Kara karanta wannan

Mun fara tattaunawa da Bankin Duniya domin karbo sabon Bashi, Shugaba Buhari

Bagudu ya kuma musanta raɗe-raɗin cewa sun gana da shugaba Buhari ne domin su shawo kansa kada ya saka hannu a kudirin dokar zabe.

Yace ganawar da suka yi da shugaban kasa kwanakin baya, sun tattauna kan babban taron APC na ƙasa dake tafe.

Zaben Anambra

Game da sakamakon zaɓen jahar Anambra, Bagudu ya bayyana shi a matsayin nasara ce ga Najeriya, ya kara da cewa dan takaran APC yana da damar faɗin matsayarsa kan zaɓen.

This Day ta rahoto Gwamnan yace:

"Zaɓe ya gudana lafiya kalau a Anambra, ina ganin Najeriya ce ta yi nasara, kuma shugaban kasa ya fitar da jawabi kan haka, muna alfahari da hukumomin tsaro."
"Kowane ɗan takarar jam'iyya a zaɓen yana da damar tsokaci kan sakamakon zaben, amma muna alfahari karkashin mulkin APC, zaben da ake ganin ba zai yuwu ba, ya yuwu."

APC ba zata tarwatse ba - Gwamnoni

Bagudu ya yi watsi da jita-jitar APC ka iya tarwatsewa duba da rikicin da yaƙi ci yaƙi cinyewa tsakanin mambobinsa, da kuma tafiyar hawainiya wajen shirya babban taro na kasa da kwamitin rikon kwarya ke yi.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Gwamnoni sun bayyana matakin da suka dauka kan kwamitin Mala Buni na APC

"Yayin da wasu jam'iyyu ke watsi da mutanen su, mu a APC muna gayyatar kowa ya jone da mu, mu sake shiri kuma mu cigaba da aiwatar da manufofin mu."

A wani labarin kuma Jigon PDP ya yi amai ya lashe, yace ya fasa tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben 2023 dake tafe

Yayin da 2023 ke kara matsowa, Attahiru Bafarawa yace ba ya sha'awar zama shugaban ƙasan Najeriya.

Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma jigo a jam'iyyar hamayya PDP yace ba zai sake neman wata kujerar siyasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262