Shekarau ya nada tsohon mataimakin Ganduje mukami bayan dawowa tsaginsa

Shekarau ya nada tsohon mataimakin Ganduje mukami bayan dawowa tsaginsa

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Shekarau ya nada wasu jiga-jigan siyasa a Kano wasu mukamai
  • Shekarau ya nada tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano da tsohon kakakin majalisar Kano a matsayin mambobin zauren shawararsa
  • Hakan ya faru ne a jihar Kano bayan da 'yan siyasar suka dawo tsagin tsohon gwamnan jihar na Kano

Kano - Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau, ya nada tsohon mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Hafizu Abubakar, da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Rt Hon Gambo Sallau, a matsayin mambobin majalisarsa na Shura.

A ranar Lahadi ne aka gabatar da wasikun nadin nasu bayan sun daidaita tare da dawowa tsagin da sanatan, Daily Trust ta ruwaito.

Shekarau ya nada tsohon mataimakin Ganduje mukami bayan dawowa tsaginsa
Tsohon gwamnan Kano, Malam Shekarau | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Majalisar ita ce mafi kololuwa wajen yanke shawara a tafiyar tsohon gwamnan jihar na Kano, wanda ya kunshi jiga-jigan fasaha da ‘yan siyasa da mutane daban-daban.

Kara karanta wannan

2023: Na fasa tsayawa takarar shugaban kasa, Jigon PDP ya yi amai ya lashe bayan nema sau 3

Abubakar ya kasance mataimakin gwamna a wa'adin farko na gwamna Abdullahi Umar Ganduje kafin ya yi murabus bisa radin kansa a shekarar 2018, gabanin zaben 2019.

A daya bangaren kuma, kafin zama kakakin majalisar a Kano, Sallau ya kasance shugaban marasa rinjaye a majalisar jihar tsawon shekaru takwas na gwamnatin Shekarau.

Da yake jawabi jim kadan bayan karbar takardar nadin nasa, Farfesa Abubakar, ya ce bai dawo tsagin tsohon Gwamna ba domin ya tsaya takarar kowane mukami a siyasance, sai dai saboda yakininsa da salon Shekarau.

Ya yi alkawarin bayar da dukkan goyon bayan da ake bukata domin samun nasarar sa.

A nasa bangaren, Sallau ya ce Shekarau ya dauke shi a matsayin shugaban marasa rinjaye a zamaninsa, duk da cewa yana jam’iyyar adawa ta PDP.

Kara karanta wannan

Labari da duminsa: Tsohon sanatan APC ya yanki jiki ya fadi, ya rigamu gidan gaskiya

A cewar Sallau:

“Ya kasance ya rike ni a matsayin Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Kano ba tare da nuna bambanci ba; wannan yana raina tun lokacin. Don haka na yi alkawarin ba zan taba barin wannan yunkuri ba."

Taron wanda ya gudana a gidan Sanatan a Kano, an shirya shi ne domin yin nazari kan halin da siyasar jihar ke ciki.

A kwanakin nan ne dai Abubakar ya dawo tsagin tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Shekarau, This Day ta ruwaito.

Jigon APC ya bayyana sirri, ya ce Buhari na goyon bayan shugaba daga yankin Igbo

A baya, Daily Trust ta ruwaito cewa, wani jigo a jam’iyyar APC kuma Darakta Janar na Voice of Nigeria (VON), Mista Osita Okechukwu, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari a sirrance yana goyon bayan a samar da shugaban Najeriya daga yankin Igbo a zaben 2023.

Da yake magana da manema labarai a ranar Lahadi a Abuja, Okechukwu ya ce shugaba daga ‘yan kabilar Igbo ne zai kawo karshen tashe-tashen hankula da barazanar kungiyar IPOB a yankin Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi a jihar Nasarawa kan kisan wasu makiyaya

A cewarsa:

“Shugaban kasa da sauran ’yan Najeriya sun yi shiru suna goyon bayan samar da shugaban Najeriya daga yankin Igbo a 2023, amma sun shuru kuma sun yi watsi da ra’ayin IPOB. Don haka, a karamar fahimta ta, tallafin da IPOB ke ba mu, zai kashe tsuntsaye biyu da dutse daya.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.