Jagoran APC a Neja ya shawarci Buhari da ya tsige Lai Mohammed daga kujerar minista
- Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Neja, Jonathan Vatsa, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tsige Lai Mohammed daga matsayin minista
- Vatsa wanda ke martani ga rahoton kwamitin bincike na Endsars ya ce ta haka ne kawai shugaban kasar zai kare martabar gwamnatinsa
- Ya gabatar da wannan bukata tasa ne a ranar Laraba, 17 ga watan Nuwamba
Neja - Tsohon kwamishinan labarai kuma jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Neja, Jonathan Vatsa, ya yi kira ga ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed da yayi murabus.
Vatsa ya kuma bukaci ministan labaran da ya bai wa 'yan Najeriya hakuri kan cewa da yayi babu wanda aka kashe a lokacin harbin toll gate, jaridar The Sun ta rahoto.
Har ila yau jigon na APC ya bayyana cewa ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsige ministan nasa idan har ya ki yin murabus da hannunsa.
A cewarsa, ta haka ne kadai shugaban kasar zai dawo da martabar gwamnatinsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Saboda haka, Vatsa ya shawarci ministan da ya ja girmansa ta hanyar mika wa shugaban kasar takardar ajiye aiki ba tare da bata lokaci ba.
Vatsa ya ce:
"Ta haka ne jinin matasa ‘yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba, wadanda jami’an tsaro suka harbe yayin da suke dauke da tutocin Najeriya da rera taken kasar, zai samu nutsuwa da shi."
A cewar tsohon sakataren na APC a jihar, rahoton kwamitin bincike ya nuna cewa lallai an yi wa matasan ’yan Najeriya masu kishin kasa kisan kiyashi a wannan dare.
Vatsa ya kuma zargi shugaban kasar da rashin ganin aibun ministocinsa.
Ya kara da cewa:
"Zuwa yanzu, kowa na sanya ran shugaban kasar zai sauya ministocinsa a lokacin da aka gane cewa tsarin bai ya aiki kwata-kwata. Iya dadewar da ya kamata ya bari su yi shine shekaru biyu."
Ya bukaci shugaba Buhari da ya ware ranar 20 ga watan Oktoba na kowani shekara a matsayin ranar tunawa da matasan 'yan Najerita da aka kashe a yayin zanga-zangar.
A bisa rahoton, Vatsa ya ce hakan zai zamo hanyar warkar da raunukan harbin da aka yi a Lekki.
EndSARS: Bayan shekara 1, bincike ya tona abin da ya faru a Lekki, an zargi Sojoji da kisan kiyashi
A wani labarin, kwamiti na musamman da gwamnatin jihar Legas ta ba alhakin binciken abin da ya faru a lokacin zanga-zangar #EndSARS ya kammala aikinsa.
VOA Hausa tace binciken kwamitin ya bada tabbacin cewa jami’an tsaro sun kashe wasu daga cikin wadanda suka yi zanga-zanga a kofar shiga Lekki.
Kwamitin da Alkali Doris Okuwobi ta jagoranta ya tabbatar da cewa sojoji sun buda wuta ga masu zanga-zanga a bakin kofar shiga wannan unguwa a Legas.
Asali: Legit.ng