Zamfara: Matawalle Na Shirin Rusa Sakatariyar Jam’iyyar PDP Bayan Ya Koma APC

Zamfara: Matawalle Na Shirin Rusa Sakatariyar Jam’iyyar PDP Bayan Ya Koma APC

  • Jam'iyyar PDP a jihar Zamfara ta garzaya kotu ta yi karar hukumar kula da tsarin birane kan barazanar rushe mata sakatariya
  • Bala Mande, shugaban riko na PDP a Zamfara ne ya bayyana hakan bayan kammala taron shugabannin jam'iyyar a Gusau
  • Mande ya bukaci yan PDP su cigaba da bin doka da oda a yayin da suka shigar da karar neman kotu ta hana rusau din tare da biyansu N60m

Jihar Zamfara - Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta ce ta shigar da kara a kotu na kalubalantar Hukumar tsare birane na Zamfara, ZUREP, saboda shirin rusa sakatariyar ta da ke Gusau.

Bala Mande, shugaban kwamitin riko na jihar, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron shugabannin jam'iyyar a sakatariyar a ranar Laraba, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin APC ya tsananta yayin da bangaren Marafa ke kokarin tsige Mai Mala Buni

Zamfara: Matawalle Na Shirin Rusa Sakatariyar Jam’iyyar PDP Bayan Ya Koma APC
Matawalle Na Shirin Rusa Sakatariyar Jam’iyyar PDP Bayan Ya Koma APC. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Mr Mande, tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamna Bello Matawalle ya cigaba da zamansa a jam'iyyar PDP bayan gwamnan ya sauya sheka zuwa APC a ranar 27 ga watan Yuni.

A cewarsa, saka maki a sakatariyar jam'iyyarsu domin a rusa ta bita da kulli ne da kuma yunkurin basu tsoro da firgita mambobin jam'iyyar da shugabanninta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mambobin jam'iyyar PDP mutane ne masu bin doka da oda kuma mun tafi kotu domin neman a bi mana hakkin mu," in ji shi.

Mr Mande, wanda tsohon kwanel ne na soja, ya bukaci magoya bayan jam'iyyar PDP su cigaba da bin doka da oda kuma su guji daukan doka a hannunsu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ta rahoto cewa cikin karar da aka shigar gaban babban kotun Zamfara a Gusau, PDP na neman kotun ta jinginar da notis din da ZUREP ta basu na ranar 29 ga watan Oktoba a kuma tabbatar saba doka ne.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya magantu kan yadda PDP za ta tsayar da dan takara

Ta kuma bukaci kotun ta tilastawa wadanda ta yi karar su biya jam'iyyar Naira miliyan 60 a matsayin tara.

‘Wanene Sarkin Cusa Kuɗi a Aljihu?’ Shekarau Ya Zolaye Ganduje Kan Bidiyon Daloli

A wani labarin, Sanata mai wakiltar Kano Central, Ibrahim Shekarau, ya caccaki gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, kan fitaccen bidiyon dalolli da ke nuna gwamnan yana soke dalolli a aljihunsa, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Ganduje ne ya fara sukar Shekarau a ranar 14 ga watan Oktoba yayin taron yan siyasa a Africa House, gidan gwamnati, a lokacin da ya zargi Shekarau da Sanata Barau Jibrin da 'karbar kudi a Abuja' ba tare da yi wa mutanensu komai ba.

https://hausa.legit.ng/siyasa/1443849-wanene-sarkin-cusa-kudi-a-aljihu-shekarau-ya-zolaye-ganduje-kan-bidiyon-daloli/

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164