2023: Tinubu ya samu gagarumin goyon bayan sarakuna 300 domin ya gaji kujerar Buhari

2023: Tinubu ya samu gagarumin goyon bayan sarakuna 300 domin ya gaji kujerar Buhari

  • Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya samu gagarumin goyon baya daga sarakunan kudu maso yamma domin zama shugaban kasa a 2023
  • Shugaban kungiyar yakin neman zaben Tinubu, Sanata Dayo Adeyeye, ya ce akalla sarakuna 300 ne suka mara masa baya domin ganin ya gaji kujerar Buhari
  • Ya bayyana Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi da Alake na Egba, Oba Adedotun Aremu cikin masu goyon bayan takarar Tinubu

Osun - Akalla sarakunan gargajiya sama da 300 daga kudu maso yamma ne ke goyon bayan takarar tsohon gwamnan jihar Lagas, Sanata Bola Tinubu, a zaben shugaban kasa na 2023.

Sanata Dayo Adeyeye, shugaban kungiyar yakin neman zaben Tinubu ne ya bayyana hakan a Gbongan, jihar Osun, rahoton Punch.

2023: Tinubu ya samu gagarumin goyon bayan sarakuna 300 domin ya gaji kujerar Buhari
2023: Tinubu ya samu gagarumin goyon bayan sarakuna 300 domin ya gaji kujerar Buhari Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Support Group Germany
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da kungiyar mai suna ‘South West Agenda for Asiwaju for 2023’ a mazabar Irewole.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan APC a Kudu sun bayyana abin da zai faru da zarar Tinubu ya zama Shugaban kasa

Adeyeye, wanda yayi kira ga mazauna yankin da su marawa kungiyar baya don yi wa Tinubu gangami ya ambaci wasu daga cikin sarakunan da suka riga suka marawa shugabancin Tinubu baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadannan sarakuna sune Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi da Alake na Egba, Oba Adedotun Aremu.

Ya ce:

“Ku wakilan SWAGA ne kuma dole ku ci gaba da yada manufar shugabancin Tinubu. Da izinin Allah, Tinubu zai zama Shugaban kasar Najeriya na gaba a 2023.
“Dukka sarakunan kasar Yarbawa suna goyon bayan Tinubu, su sama da 300 ke goyon bayansa. Daga Ooni na Ife zuwa Alaafin na Oyo, Alake da sauransu. Shine dan takara mafi cancanta da zai fito daga kasar Yarbawa.”

Da yake magana, jagoran kungiyar SWAGA a jihar Osun, Ayo Omidiran, ya ce baya ga goyon bayan Tinubu gabannin zaben shugaban kasa na gaba, kungiyar na goyon bayan Gwamna Adegboyega Oyetola, gabannin zaben gwamnan 2022.

Kara karanta wannan

Basarake ya gwangwaje diyarsa da kyautar mota bayan ta kammala digiri da daraja ta farko

2023: Jagoran APC Bola Tinubu ya samu gagarumin goyon bayan mutum 50,000 a wannan jiha

A wani labarin, tsohon shugaban ma'aikata na gidan gwamnatin jihar Ribas, Chief Tony Okocha, yace shugabannin APC a jihar sun fara shirin haɗa mambobi 50,000 domin goyon bayan Tinubu.

Leadership ta rahoto cewa zasu haɗa waɗan nan mutanen ne domin nuna goyon bayansu ga jagoran APC, Bola Tinubu, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Okocha, wanda ya rike mukamin shugaban ma'aikata lokacin mulkin tsohon gwamna, Rotimi Amaechi, ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da manema labarai a Patakwal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng