Fastocin kamfe na Sanata Kalu sun yadu a kudu, zai tsaya takarar shugaban kasa a APC

Fastocin kamfe na Sanata Kalu sun yadu a kudu, zai tsaya takarar shugaban kasa a APC

  • Fastocin kamfen na Sanata Orji Kalu, na takarar shugaban kasa a zaben 2023 sun karade Umuahia
  • A bisa ga fastocin, Kalu zai nemi kujerar Shugaba Buhari ne a karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC)
  • Sai dai kuma, hadimin Kalu, Maduka Okoro, ya bayyana cewa ba daga ofishin tsohon gwamnan fastocin suka fito ba

Jihar Abia - Fastocin kamfen na bulaliyar majalisar dattawa, Orji Kalu, na takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun karade Umuahia.

An gano fastocin dauke da rubutun "ku zabi Dr Uzor shugaban kasa - Sabuwar Najeriya ta zo" a manyan gine-ginen da ke shataletalen Abia, a babban titin Enugu-Port Harcourt.

Fastocin kamfe na Sanata Kalu sun yadu a kudu, zai tsaya takarar shugaban kasa a APC
Fastocin kamfe na Sanata Kalu sun yadu a kudu, zai tsaya takarar shugaban kasa a APC Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Fastocin wadanda aka bayyana cewa matasan arewa ne suka buga shi yana dauke da wasu batun da ke bayyana Mista Kalu a matsayin 'shahararren dan siyasa', 'mai gina kasa' da kuma 'mutumin da zai ceto tattalin arziki'.

Kara karanta wannan

Har bayan wata 7, an kasa sasanta rikicin Kwankwaso da Wali a PDP

Da yake martani a kan ci gaban, hadimin Kalu, Maduka Okoro, ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa ba daga ofishin tsohon gwamnan na Abia fastocin suka fito ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mista Okoro ya ce tsohon gwamnan bai ayyana aniyarsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ba, rahoton Premium Times da The Nation.

Ya bayyana hakan a matsayin aikin masoyan Mista Kalu saboda kyakkyawan aikin da yake yi ko kuma aikin wasu masu nufi na daban.

Ya ce:

"Ba mu lika fastocin Sanata Orji Uzor Kalu a ko’ina ba. Ba mu yi tunani kan haka ba kuma ba mu yi wata magana ta musamman kan haka ba.
"Mun mayar da hankali wajen kafawa mutanenmu tarihi- gyara makarantu, gina hanyoyi da sauran ayyuka, domin mutanenmu su sha romon damokradiyya."

Ya bayyana cewa Kalu, mai wakiltan Abia ta arewa a majalisar dattawa, zai gabatar da jawabi ga manema labarai idan yana da wannan kudiri.

Kara karanta wannan

Hotuna da sunayen jaruman Sojojin da aka kashe a artabu da yan ta'adan ISWAP

Shugaban kasa a 2023: Matasan arewa sun nuna goyon bayansu ga shahararren dan siyasar kudu

Legit Hausa ta kawo a baya cewa wata kungiya ta matasan arewa karkashin inuwar Arewa Youths for Orji Uzor Kalu ta nuna goyon bayanta ga bulaliyar majalisar dattawa, domin zama shugaban kasa na gaba.

Kungiyar ta bayyana matsayinta ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa dauke da sa hannun jagoranta na kasa, Yakubu Muhammad; mukaddashin sakatarenta, Abdulkadir Muhammad; sakataren shirye-shirye, Ibrahim Abdullahi, da kuma daraktan labaranta, Musa Waziri.

A cikin sanarwar da aka fitar a Abuja a ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba, sun bayyana Kalu a matsayin wanda ya fi cancanta da zama shugaban kasa a babban zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng