2023: Mika shugabancin Najeriya ga Igbo zai kawo karshen fafutukar IPOB, Ohanaeze, MBF
- Kungiyar mutanen kudu maso gabashin Najeriya, Ohanaeze Ndigbo, tace baiwa ɗan Igbo shugabancin Najeriya ne zai kawo karshen IPOB
- Hakanan kuma kungiyar MBF ta nuna goyon bayanta ga kiran Ohanaeze game da ɗan Igbo ya ɗare kujera Lamba ɗaya a 2023
- A cewar kungiyoyin biyu, rashin daidaito tsakanin dukkan yankunan ƙasar nan ne ke haifar da irinsu IPOB
Abuja - Kungiyar inyamurai ta ƙasa, Ohanaeze Ndigbo, da kuma kungiyar Middle Belt Forum (MBF) sun bayyana cewa samar da shugaban ƙasa Igbo ne kaɗai zai kawo karshen fafutukar IPOB.
Leadership tace wannan na zuwa ne bayan kungiyar PANDEF dake kudu maso kudancin Najeriya tace ba ta adawa da ɗan Igbo ya jagoranci Najeriya.
A cewar PANDEF matukar an maida shugabancin ƙasar nan kudu a 2023, to ba ta adawa da koma waye ya zama shugaban ƙasa, kamar yadda Punch ta rahoto.
Shin haka zai haifar da sakamako mai kyau?
Shugaban matasan Ohanaeze na duniya, Mazi Damian Okafor, ranar Lahadi, yace da zaran Igbo ya zama shugaban ƙasa, fafutukar ballewa zata zo ƙarshe a yankin kuma zaman lafiya zai dawo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mazi Okafor ya bayyana cewa shugaba Olusegun Obasanjo, ya kawo ƙarshen masu fafutukar kafa Oduduwa, kuma gwamnatin marigayi Yar'adua ta yi kokarin kawo karshen Boko Haram.
Yace:
"Na yi imanin cewa idan aka baiwa Igbo damar jagorancin ƙasar nan, duk wannan fafutukar yan awaren zata ƙare. Ya kamata a yi wa Igbo adalci kamar sauran yankuna."
"Mun cancanci kujera mai lamba ɗaya, kuma hakan zai kawo ƙarshen matsalar yan aware. Lokaci ya yi da zamu sami abinda kowane yanki yake samu."
"Mun taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasar nan, kuma ya dace a bamu kujerar shugaban ƙasa."
Menene hangen MBF?
A nata ɓamgaren kungiyar MBF, ta nuna goyon bayanta ga kiran Ohanaeze Ndi-Igbo na ɗan kabilar Igbo ya shugabanci Najeriya a 2023.
Ta kuma kara da cewa samar da ɗan Igbo a matsayin shugaban ƙasa zai kawo karshen masu fafutukar ballewa a yankin.
Da yake zantawa da Leadership ranar Lahadi, Shugaban MBF na ƙasa, Dakta Bitrus Pogu, yace rashin tsarin daidaito a ƙasa ne ya haifar da yan fafutukar ballewa.
Yace:
"Mun daɗe muna faɗa cewa rashin daidaito a tsarin Najeriya ne ya haifar da waɗan nan masu fafutukar ballewa daga ƙasa."
"Saboda haka ne muke ƙara jaddada cewa wajibi ne a zauna a sake fasalin ƙasar nan matukar ana son cigaba. Abinda Ohanaeze ke faɗa yana kan maganar sake fasalin kasa."
"Ina da yaƙinin cewa fafutukar ballewa zata ƙare, ba wai a kudu maso gabas ba kaɗai, har da sauran yankuna. Son rai yasa ake wannan rashin daidaiton."
A wani labarin kuma Saraki ya yi magana kan kudirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 da shirin sauya sheka daga PDP
Tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Abubakar Bukola Saraki, yace yanzun ba ya tunanin kansa a siyasar Najeriya.
Saraki yace a halin yanzun fatan sa shine PDP ta shawo kan matsalolinta, ta zama tsintsiya ɗaya domin ceto Najeriya daga hannun APC.
Asali: Legit.ng