Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya magantu kan yadda PDP za ta tsayar da dan takara

Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya magantu kan yadda PDP za ta tsayar da dan takara

  • Sabon shugaban jamiyyar PDP ya magantu kan yadda jam'iyyar za ta bi wajen tsayar da dan takara a 2023
  • Ya bayyana cewa, jam'iyyar ta dimokradiyya ce, kuma za ta bi hanyoyin da suka dace wajen tsayar da dan takararta
  • Ya kuma tabbatar da cewa, jam'iyyar za ta iya bin tsarin gabatar da shiyya don tsayar da dan takara kamar yadda tayi a shugabancin jam'iyyar

Farfesa Iyorchia Ayu, sabon shugaban jam'iyyar PDP na kasa ya magantu kan matsayar jam'iyyar wajen tsayar da dan takara gabanin zaben shugaban kasa mai zuwa na 2023.

Shugaban na PDP ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta musamman da jaridar Daily Trust a karshen makon nan.

Shiyyoyin siyasar kasar nan sun sha bayyana ra'ayoyinsu kan yankin da ya kamata ya fitar da dan takarar shugaban kasa a dukkan jam'iyyun siyasa, lamarin da ya jawo cece-kuce daga bangarori daban-daban.

Kara karanta wannan

2023: Abin da jam'iyyar PDP za ta yi idan APC ta tsayar da Jonathan matsayin ɗan takara, Tambuwal

Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya magantu kan yadda PDP za ta tsayar da dan takara
Sabon shugaban PDP, Iyochia Ayu | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A hirar da aka yi da Ayu, Daily Trust ta tambaye shi kan matsayar jam'iyyar PDP kan ci gaba da tsayar da shiyya ga wata kujera ganin matsalolin da ke cikinta, ya amsa da cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mu jam'iyya ce mai matukar bin dimokradiyya. Ba mu da matsala wajen magance matsalolinmu a cikin jam’iyyarmu."

Ya kuma bayyana yadda mutane da yawa suka yi zaton karshen PDP yazo lokacin da ta yanke shawarar rarraba kujerun shugabancin jam'iyyar ga shiyyoyin siyasa.

A cewarsa:

"Kowa ya dauka cewa ba da ofisoshin jam’iyya ga shiyya zai ruguza jam’iyyar PDP. Ina jin 'yan Najeriya sun yi mamakin yadda muka warware ba tare da wata jayayya ba. Don haka wadanda ke kawo rigingimu a jam’iyyar ba su samu abinda suke so ba.

Hakazalika, ya tabbatar da cewa, jam'iyyar a shirye take ta dauki matakai na dimokradiyya wajen tsayar da 'yan takara ko yanke shawara a cikinta.

Kara karanta wannan

Kungiyar PDP ta nemi Gwamna Wike ya nemi takarar kujerar shugaba Buhari a 2023

Ya kara da cewa:

"Idan lokaci ya yi za mu mika kanmu ga wani tsarin na dimokradiyya. Kuma za mu fito da dan takarar da zai yi nasara.
"Na yi imanin 'yan Najeriya za su yi farin ciki da abin da za mu fitar musu a cikin 'yan watanni masu zuwa."

Bayan lashe zabe, sabon shugaban PDP ya mika zazzafan sako ga jam'iyyar APC

A baya, sabon zababben shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya aike da sako ga jam'iyyar APC mai mulki, yana mai cewa “zamu karbe kasar nan.”

Da yake magana da sanyin safiyar Lahadi bayan zaben sa a taron gangamin jam’iyyar na kasa a Abuja, Ayu ya bayyana shirin jam'iyyar na karbe mulkin kasar a zaben 2023, This Day ta ruwaito.

A cewarsa:

“Nan da makonni biyu za ku ga karfin da zai dawo PDP a kowace jiha. Wasu tsirarun mutane sun yanke shawarar raba Najeriya. Za mu hada kan kasar don ci gaban kasar nan.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra 2021: Dalilai 4 da ka iya sa Charles Soludo na APGA ya lashe zabe

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.