Da dumi-dumi: INEC ta gabatarwa da Soludo takardar shaidar lashe zaben Anambra
- Hukumar INEC ta mika takardar shaidar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo
- An mika wa Soludo takardar ne a wani taro da aka gudanar a garin Awka, babbar birnin jihar a ranar Juma'a, 12 ga watan Nuwamba
- Soludo, dan takarar jam'iyyar APGA ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra da aka gudanar a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba
Awka, Jihar Anambra - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta gabatar da takardar shaidar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo.
Hukumar INEC ta ayyana Soludo, wanda ya kasance dan takarar jam'iyyar All Progressives Grand Alliace, APGA, a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba.
2023: Masu neman takarar gwamna 7 daga APC da PDP na shirin sauya sheka zuwa APGA a wata jihar kudu maso gabas
An gudanar da taron gabatar masa da takardar ne a Awka, babbar birnin jihar a yau Juma'a, 12 ga watan Nuwamba, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu zabe na kasa Festus Okoye, wanda ya gabatar da takardar lashe zaben ga Soludo, ya ce gabatar da takardar ya cika sharuddankundin tsarin mulki na dokar zabe, rahoton TVC News.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dan takarar gwamnan PDP ya amince da shan kaye, ya taya Soludo murna
A gefe guda, mun kawo a baya cewa dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan Anambra da aka kammala, Valentine Ozigbo, a ranar Laraba ya amince da shan kaye tare da taya dan takarar jam’iyyar APGA, Chukwuma Soludo murnar lashe zabe, Punch ta ruwaito.
Soludo mai shekaru 61 ya samu nasara da kuri’u 112,229 inda ya doke Ozigbo wanda ya samu kuri’u 53,807 da Andy Uba na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 43,285 da kuma Ifeanyi Ubah na jam'iyyar YPP da ya samu kuri'u 21,261 wanda ya zo na hudu.
Ozigbo, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce:
"Yanzu na kira Farfesa Chukwuma Soludo na kuma taya shi murnar ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra, 2021. Ina yi masa fatan alheri da kuma yi masa addu'ar samun nasara."
Asali: Legit.ng