An shigar da Hafsat Barauniya kotu kan amsar kudi amma taki yin aikin

An shigar da Hafsat Barauniya kotu kan amsar kudi amma taki yin aikin

  • Sabuwar takaddama a masana'antar Kannywood tsakanin wani kamfani da yar wasa Hafsat Idris
  • UK Entertainment ta bayyana cewa ta biya Hafsat Idris kudi sama da milyan daya don ta fito wani shirin Fim amma ta ki fitowa
  • Kamfanin ya ce yayi asara sakamakon rashin cika alkawarin Hafsat

Kano - Wani kamfanin shirya wasan kwaikwayo, UK Entertainment, ya shigar da shahrarriyar jarumar Kannywood, Hafsat Idris, wacce akafi sani da Barauniya, kotu a jihar Kano.

Kamfanin ya tuhumi Hafsat da saba alkawarin dake tsakaninsu bayan yarjejeniyar da sukayi, DailyTrust ta ruwaito.

An shigar da ita kara gaban babbar kotu a jihar Kano dake zamanta a karamar hukumar Ungogo.

A cewar karar, an tuhumi yar wasar da karban kudi N1.3 million don ta fito a wani shirin Fim amma taki fitowa duk da yarjejeniyar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatan kananan hukumomi 13

Kamfanin ya bayyanawa kotu cewa ya yi asara matuka kan wannan abu da jarumar tayi kuma yana bukatar ta biyashi kudin saba alkawari N10 million.

Lauyan Hafsat Idris, ya bukaci martani kan wannan lamari.

An dage zaman.

An shigar da Hafsat Barauniya kotu kan amsar kudi amma taki yin aikin
An shigar da Hafsat Barauniya kotu kan amsar kudi amma taki yin aikin
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel