Fidda gwani kai tsaye: PDP ta magantu, ta ce za ta bayyana matsayar ta nan kusa
- Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana lokacin da za ta bayyana matsayar ta kan sabuwar ka'idar shigar da zaben fidda gwani
- PDP ta ce duk wata jam'iyya tana da dokokin cikin gida da ya kamata a bar mata ta ci gaba da ji da su yadda taso
- Saboda haka, jam'iyyar PDP ta bayyana cewa, za ta fadi matsayar ta kan wannan sabon tsari nan da wani dan lokaci
Abuja - Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce za ta bayyana matsayarta kan tsarin daidaita dokar zabe nan da sa’o’i 48, Daily Sun ta ruwaito.
Jam’iyyar PDP wadda tun da farko ta nuna rashin amincewa da shigar da zaben fidda gwani kai tsaye, ta ce kowace jam’iyyar siyasa tana da ‘yancin tantance yadda za ta zabi ‘yan takararta.
Jam’iyyar adawar a cikin wata sanarwa da kakakinta, Kola Ologbondiyan ya fitar, ta ce babu wata jam’iyyar siyasa da ke da hurumin kakaba tsarin zaben fidda gwani a kan wata jam’iyya.
A cewar sanarwar:
“Jam’iyyarmu ta amince da cewa, hakkin kowace jam’iyyar siyasa ne, bisa tsarin mulkin dimokuradiyyar kasar nan, ta yanke shawarar yadda za ta gudanar da ayyukanta na dimokuradiyya a cikin gida ciki har da tsarin tantance ‘yan takararta a zabe a kowane mataki.
"Jam’iyyar PDP ta kuma yi imanin cewa, babu wata jam’iyyar siyasa da za ta tilasta wa wata jam’iyyar siyasa ta aiwatar da tsarinta, a matsayin gyaran da aka yi na zaben fidda gwani kai tsaye, al’adar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ke neman cimmawa.
"Bayan da PDP ta bayyana hakan, nan da sa’o’i 48 masu zuwa, za ta yanke hukuncin karshe game da wannan gyara.”
Me ya faru da PDP a baya-bayan nan?
A baya-bayan nan ne jam'iyyar PDP ta gudanar da taron gangamin na kasa, wanda aka gama lafiya tare da fitar da sakamako mai kyau.
Taron ya gudana duk da tsaiko da ya samu daga korarren shugaban jam'iyyar na kasa Uche Secondus, inda aka zabe sabbin shugabannin jam'iyya.
Jam'iyyar ta gudanar da zaben shugabanni, inda ta zari Iyorchia Ayu a matsayin sabon shugabanta, BBC ta ruwaito.
Zaben Anambra: Dalilai 5 da suka sa PDP ta sha mummunan kaye a zaben gwamna
Kunji cewa, a zaben Anambra, dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP Valentine Ozigbo ya lashe karamar hukuma daya kacal a kada kuri'a da aka yi.
Ozigbo ya samu kuri’u 3,445 inda ya doke Chukwuma Soludo, dan takarar jam’iyyar APGA, wanda ya samu kuri’u 3,051, yayin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu kuri’u 1,178 a karamar hukumar Ogbaru.
Wannan shine nasara ta farko da PDP ta samu a tsakanin kananan hukumomin jihar da aka kada kuri'a a zaben na gwamna.
Asali: Legit.ng