Zaben Anambra: Soludo ya shiga sahun su Ganduje, gwamnonin Najeriya masu PhD
- Yanzu dai ba sabon labari ba ne cewa Farfesa Chukwuma Charles Soludo na jam’iyyar APGA shi ne zababben gwamnan jihar Anambra
- An bayyana Farfesan mai shekaru 61 a fannin tattalin arziki kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya a matsayin wanda ya lashe zaben da aka kammala a Anambra
- Yanzu haka Farfesa Charles Chukwuma Soludo shine zababben gwamna na shida a Najeriya a wannan zangon siyasa na yanzu da ya samu digirin digirgir
Awka, Anambra - Zababben gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Charles Soludo ya shiga littattafan tarihin Najeriya yayin da ya shiga jerin gwamnonin da a halin yanzu suke da digirin dgirgir (PhD).
Yawancin ‘yan siyasar Najeriya ba a san su da yin fice a fannin ilimi ba, amma labarin ya fara canjawa a cikin shekaru goma da suka gabata.
Soludo ya shiga cikin jerin fitattun kwararrun da suka yi fice a harkar kasuwanci kafin shiga cikin fafutukar siyasar Najeriya.
Soludo, mamba ne a kungiyar masu ba da shawara ta kasa da kasa ta sashen ci gaban kasa da kasa ta Burtaniya, a halin yanzu mamba ne a kwamitin ba da shawara kan tattalin arziki mai mutane 8 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a watan Satumban 2019.
Soludo ya kasance malami mai ziyara a Asusun Ba da Lamuni na Duniya, Jami'ar Cambridge, Cibiyar Brookings, Jami'ar Warwick, da Jami'ar Oxford da kuma Farfesa mai ziyara a Kwalejin Swarthmore da ke Amurka.
Ya kuma yi aiki a matsayin mai ba da shawara ga kungiyoyin kasa da kasa da dama, da suka hada da Bankin Duniya, da Hukumar Tattalin Arziki ta Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Afirka, da kuma shirin raya kasashe na Majalisar Dinkin Duniya.
Ya yi digirinsa na digirgir sannan ya zama Farfesa a Jami'ar Najeriya da ke Nsukka, jihar Enugu. Ya kammala karatunsa na digiri na farko a 1984, MSc a fannin tattalin arziki a 1987, sannan ya yi Ph.D. a 1989, ya lashe kyaututtuka na dalibi mafi kwazo a dukkan matakan uku.
Sauran gwamnoni biyar da a halin yanzu suke da Ph.D. sun hada da:
- Dr. Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano
- Dr. John Kayode Fayemi na jihar Ekiti
- Farfesa Benedict Ayade na jihar Kuros Riba
- Farfesa Babagana Zulum na jihar Borno da
- Dr. Okezie Ikpeazu na jihar Abia
Dalla-dalla: Yadda Soludo ya lashe zabe a LGAs 19, ya lallasa Uba, Ozigbo da sauransu
A wani labarin, Farfesa Charles Soludo, dan takarar gwamnan jihar Anambra karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ya bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 6 ga watan Nuwamba.
Manyan abokan hamayyar Soludo a zaben su ne Andy Uba na jam'iyyar APC, Valentine Ozigbo na jam'iyyar PDP da Ifeanyi Ubah na jam'iyyar YPP.
Ga dalla-dallar yadda tsohon gwamnan babban bankin Najeriyan ya lallasa sauran 'yan takara tare da samun nasara.
Asali: Legit.ng