KAI TSAYE: Dan takarar APGA, Charles Soludo ya tabbata zababben gwamnan Anambra

KAI TSAYE: Dan takarar APGA, Charles Soludo ya tabbata zababben gwamnan Anambra

Kamar yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta sanar cewa a yau Talata za'a gudanar da ƙarishen zaben gwamnan Anambra wanda bai kammala ba ranar Asabar.

Punch tace An gudanar da wannan zaben a ƙaramar hukumar Ihiala, yankin da INEC ta tabbatar ba'a gudanar da zabe ba sam.

Idan kuma biye da mu, mun kawo muku yadda ta wakana a rumfunan zaɓe dake wannan karamar hukuma, kuma a halin yanzu sakamako ya fara fita.

Ku cigaba da bibiyar mu, yayin da wakilan mu suke can Anambra domin kawo muku rahotannin sakamakon wannan zaɓe da aka fafata yau.

Dan takarar APGA, Charles Soludo ya tabbata zababben gwamnan Anambra

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta bayyana Farfesa Chukwuma Soludo a matsayin zababben gwamnan jihar Anambra.

Farfesa Florence Obi, baturiyar zaben jihar, ta bayyana hakan wurin karfe 1;50am na safiyar Laraba, Daily Trust ta wallafa.

KAI TSAYE: Dan takarar APGA, Charles Soludo ya tabbata zababben gwamnan Anambra
KAI TSAYE: Dan takarar APGA, Charles Soludo ya tabbata zababben gwamnan Anambra. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

An cigaba da tattara sakamako a Awka

Da misalin ƙarfe 9:25 na dare, baturen zaɓen gwamnan Anambra, Florence Obi, ta zauna tare da sauran jami'an hukumar INEC, yayin da ake dakon isowar sakamakon Ihiala.

Ana tsammanin an gudanar da zaɓe a runfunan zaɓe 326 dake faɗin ƙaramar hukumar Ihiala a yau Talata.

Waɗan nan rumfunan zabe ne zasu tantance wanda zai jagoranci jihar Anambra a shekaru hudu masu zuwa.

Dakin tattara sakamako
KAI TSAYE: Sakamakon zaben gwamna daga Ihiala a Anambra ya fara isowa Hoto: thecable.ng
Source: UGC

Za a ci gaba da tattara sakamakon zabe da misalin karfe 9 na dare

Nkwachukwu Orji, kwamishinan zabe na INEC a jihar, ya sanar da manema labarai cewa, za a ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Anambra da misalin karfe tara na dare.

Wurin dai shi ne cibiyar tattara sakamakon zabe na Jiha wato ofishin INEC na jihar, daura da titin majalisar dokoki, Awka.

Sakamakon gundumar Uli 1

Runfar zaɓe ta 004

APGA -13

APC - 4

PDP - 19

LP - 1

Runfar zaɓe: 014

APGA -20

PDP -19.

YPP -1

APC - 2

Online view pixel