Da Dumi-Dumi: Dan majalisar tarayya ya fice daga jam'iyyar hamayya, ya koma APC mai mulki

Da Dumi-Dumi: Dan majalisar tarayya ya fice daga jam'iyyar hamayya, ya koma APC mai mulki

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta yi babban kamu a majalisar dokoki, inda wani ɗan majalisa ya sauya sheka zuwa APC
  • Kakakin majaisar wakilai, Femi Gbajabiamila, shine ya sanar da sauya shekar Ajao Adejumo, daga ADP zuwa APC
  • Guguwar sauya sheƙa ta yi gaba da yan majalisan wakilai 20 zuwa APC cikin watanni 11 kacal, mafi yawa daga PDP

Abuja - Ɗan majalisar wakilan tarayya, Ajao Adejumo, ya fice daga jam'iyyar hamayya ADP, ya koma jam'iyyar APC mai mulki.

Kakakin majaisar wakilai, Femi Gbajabiamila, shine ya sanar da matakin sauya shekan Adejumo, ranar Talata a zauren majalisa, bayan dawowa daga hutu.

The Cable tace majalisar wakilai ta dakatar da zamanta ne mako uku da suka gabata domin baiwa kwamitocinta damar gudanar da aikinsu kan kasafin kudin 2022.

Jam'iyyar APC
Da Dumi-Dumi: Dan majalisar tarayya ya fice daga jam'iyyar hamayya, ya koma APC mai mulki Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Meyasa ya koma APC?

Kara karanta wannan

Zaben Anambra 2021: Dalilai 4 da ka iya sa Charles Soludo na APGA ya lashe zabe

Adejumo, wanda ke wakiltar mazaɓar Ogbomoso north/Ogbomosho south/Oriire a majalisar dokokin tarayya daga jihar Oyo, yace ya koma APC ne domin ɗaga martaban Najeriya.

A jawabinsa yace:

"Kyakkyawan jagorancin ka (Kakakin majalisa), tsarinka da kuma jawo kowa a jiki wajen gudanar da shugabancinka ne ya jawo hankali na zuwa gare ka da APC domin ɗaga Najeriya zuwa gaba."

Guguwar sauya sheka

Ana cigaba da samun masu sauya sheƙa a majalisar dokokin tarayyan Najeriya cikin makonni kaɗan da suka gabata.

Legit.ng Hausa ta gano cewa jam'iyyar APC mai mulki ta samu ƙarin yan majalisu 20 da suka shigo cikinta cikin watanni 11 da suka shuɗe.

Bugu da ƙari, mafi yawan waɗan nan yan majalisu dake sauya sheƙa suna fitowa ne daga babbar jam'iyyar hamayya PDP.

Kara karanta wannan

Gwamnan Yobe zai gana da wasu jiga-jigan APC don dinke barakar APC a jihar Oyo

A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar APC ta maida martani kan zargin da ake mata game da zaben gwamna a jahar Anambra

Jam'iyyar APC ta musanta jita-jitar da ake jingina mata cewa ta bukaci hukumar INEC ta soke zaɓen Anambra.

Shugaban APC reshen Anambra, Chief Basil Ejidike, yace ba dalilin da zai sa APC ta faɗi haka yayin da ake cigaba da zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262