Rahoto: INEC ta tabbatar da batun sace akwatin zabe a wasu rumfuna a zaben Anambra
- Rahotanni sun yi yawo a kafafen yada labarai cewa an yi satar akwatin zabe a wasu rumfunan zabe a jihar Anambra
- Hukumar INEC ta tabbatar da faruwar haka, ta ce ana tabbas an yi haka, kuma ta bayyana sunan karamar hukumar
- A halin yanzu an tafi hutun wani dan lokaci daga baya za a dawo don ci gaba da sauraran sakamakon zabe daga INEC
Anambra - Premium Times ta ruwaito cewa, kwamishinan hukumar zabe na INEC a jihar Anambra, Nwachukwu Orji, ya tabbatar da rahotannin tarzoma da sace-sacen akwatin zabe a wasu rumfunan zabe a jihar.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a gidan Talabijin na Channels a ranar Asabar.
Mista Orji ya ce an samu rahotannin sace akwatin zabe a wasu rumfunan zabe a karamar hukumar Idemili.
Hukumar ta ce ‘yan daba sun yi awon gaba da akwatunan zabe sama da bakwai dauke da daruruwan kuri'un zabe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
“Akwai matsalar sace kuri’a a lokacin zaben. Wasu ‘yan daba ne suka zo suka kawo cikas, suka kwashe akwatunan zabe.
“Hakan ya faru ne a Idemili Arewa da Kudu. Kimanin akwati bakwai aka kwashe.”
Mista Orji ya kuma ce akwai wuraren da aka hana jami’an INEC shiga, lamarin da ya kawo tsaikon gudanar da zaben. Sai dai ya ce ba zai dauki hakan a matsayin babban kalubalen tsaro ba.
Ya kara da cewa:
“Ba zan yi la’akari da shi a matsayin babban kalubalen tsaro ba saboda zaben ya kasance cikin kwanciyar hankali. Abin mamaki ne ga mutane da yawa kasance cikin kwanciyar hankali duba da barazanar tsoron hari da duka."
Da aka tambaye shi ko za a soke kuri'u a yankunan da abin ya shafa, ya ce "wannan shawara ce da za a yanke daga baya amma a yanzu dole ne a kammala aikin."
INEC ta karbi sakamakon zaben kananan hukumomi 19 cikin 21
A wani labarin, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da karbar sakamakon zaben kananan hukumomi 19 na jihar daga cikin 21, The Nation ta ruwaito.
Sauran biyun kuma a cewar Hukumar ana dakon su kuma za su isa Hukumar da ranar yau din nan.
Mista Festus Okoye, kwamishinan INEC na kasa, mai kula da kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a ne ya sanar da hakan da safiyar Lahadi a ofishin hukumar da ke Awka.
Asali: Legit.ng