Yanzu-yanzu: Gwamnan Anambra ya saki jerin kananan hukumomi 10 da APC ta rubuta sakamakon zaben tun kan a fara

Yanzu-yanzu: Gwamnan Anambra ya saki jerin kananan hukumomi 10 da APC ta rubuta sakamakon zaben tun kan a fara

  • Ana gab da da fara zabe a jihar Anambra, gwamnan jihar ta saji jawabin da yake zargin jam'iyyar APC da magudi
  • Obiano wanda ya zama Gwamna karkashin jam'iyyar APGA yace kananan hukumomi 10 mafi jama'a akayi hakan
  • Jam'iyyar APC ta yi kira ga Gwamnan ya daina kokarin tunzura mutane da kuma tayar da hayaniya

Awka, Anambra state - Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya yi kuka kan yadda jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta shirya sakamakon zabe a kananan hukumomi goma tun kan a fara zabe.

Obiano ya bayyana hakan da yammacin Juma'a, 5 ga Nuwamba ta bakin Kwamishanan yada labaran jihar, C Don Adinuba, TheNation ta ruwaito.

Ga jerin kananan hukumomin da yayi zargin tuni an rubuta sakamakonsu:

1. Onitsha North

2. Onitsha South

Kara karanta wannan

Da duminsa: Soludo ne a sahun gaba, APGA ta lashe kananan hukumomi 16 a Anambra

3.Aguata

4. Orumba South

5. Orumba North

6. Idemili North

7. Idemili South

8. Ogbaru

9. Anambra East

10. Anambra West

jerin kananan hukumomi 10 da APC ta rubuta sakamakon zaben tun kan a fara
Yanzu-yanzu: Gwamnan Anambra ya saki jerin kananan hukumomi 10 da APC ta rubuta sakamakon zaben tun kan a fara Hoto: Anambra State Governemnt
Asali: Facebook

Zaben gwamna: Gwamnati ta karyata rahoton cewa mutane na tururuwan barin Anambra

Kwamishinan labarai da wayar da kan jama'a na jihar Anambra, Mista Don Adinuba, ya ce rahoton da ke yawo na cewa mutane na tururuwan barin jihar yayin da ake zaben gwamna karya ne.

Adinuba ya bayyana cewa maimakon haka, mutane na shigowa cikin jihar kwansu da kwarkwatarsu, musamman wadanda suka cancanci yin zabe domin shiga sahun masu kada kuri'a a zaben gwamnan wanda ke gudana a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba.

Ya magantu a kan lamarin ne a cikin wata sanarwa, wanda aka aike wa kamfanin dillancin labaran Najeriya a safiyar ranar Asabar a garin Awka, babbar birnin jihar.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Soludo ya lashe karamar hukumar Anaocha, mahaifar 'yan takara uku

Ya bayyana cewa an ja hankalin gwamnatin jihar a kan rahoton labaran wanda ke ikirarin cewa mutane na barin Anambra saboda tsoron rikicin siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng