Tituna sun yi wayam babu kowa yayin da mazauna Anambra suka fara zaman gida duk da soke umurnin da IPOB ta yi
- Gabannin zaben gwamna na ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba, harkoki sun tsaya cak a jihar Anambra
- Mutane sun bi umurnin zaman gida da kungiyar awaren IPOB ta kafa duk da cewar daga bisani ta soke shi
- Wurare da dama dake da yawan hada-hadar jama'a a babban birnin jihar kamar Unizik Junction, Ifite, Okpuno Agu Awka sun zama tamkar kufai
Anambra – A yayin da ake shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Anambra a gobe Asabar, 6 ga watan Nuwamba, yawancin unguwanni a jihar sun yi tsit babu kowa yayin da mazauna yankin suka shige gida saboda dokar zaman gida na sati guda.
Duk da cewar kungiyar awaren IPOB ta soke umurnin a yammacin ranar Alhamis, 4 ga watan Nuwamba, mazauna jihar sun ki fitowa saboda tsoron kada a far masu ko kuma a ci zarafin su.
Yanzu-yanzu: Ƙungiyar IPOB ta saduda, ta soke dokar zaman gida na dole, ta ce a fita a yi zaɓe a Anambra
Wakilin Legit.ng wanda ya ziyarci wurare da dama dake da yawan hada-hada a babban birnin jihar kamar Unizik Junction, Ifite, Okpuno Agu Awka ya lura cewa harkokin kasuwanci sun tsaya cak a yankin.
Mai sana'ar siyar da abinci ta koka
Ogechi Anyanwu, wata mai siyar da abinci a mararrabar UNIZIK wacce ta yi ta maza ta fita siyar da abinci, ta yi korafi a kan rashin kwastamomi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta ce:
"Ina fitowa a kullun da misalin karfe 6:00 na asubahi. Dukka masu adaidaita a wurina suke siyan abinci har ta kai kafin karfe 8:00 na safe abincina ya kare.
"Ga shi yanzu basu fito ba, ban san me zan yi da abincin nan ba yanzu.
"Kuma na ji labarin soke dokar zaman gidan a daren jiya. Amma har yanzu mutane suna tsoron fitowa. Wannan abun bakin ciki ne."
Na zata mutane za su fiffito
Nnaemeka Odogwu, wani direban adaidaita a yankin Ifite na Awka, ya yi mamakin dalilin da ya hana mutane fitowa duk da soke dokar na IPOB.
Ya ce:
"Na yi zaton mutane za su fito a safiyar yau bayan mun ji cewa an soke umurnin a daren jiya.
"Na fito da tunanin za a samu yawan zirga-zirga. Koda dai ina zama ne a yankin. Na cika da mamakin ganin cewa har yanzu mutane sun ki fitowa. Na san duk tsoro ne. Amma ba zai yiwu mu ci gaba da zama a haka ba."
Wani dan jarida da ke zaune a Awka wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Legit.ng cewa al’amura na iya komawa daidai zuwa anjima.
"Ina ganin jawabin IPOB ya zo a kuraren lokaci. Watakila suna tattaunawa da masu madafun iko ne.
“Wasu mutane ma suna da shakku ko da gaske furucin ya fito ne daga kungiyar IPOB, amma zan iya tabbatar da cewar hakan ya fito daga gare su ne.
"Amma zan iya bayar da tabbacin cewa lamura za su daidaita zuwa anjima. Idan ka lura mutane na fitowa daya bayan daya. Abun na dan lokaci ne kafin saura su fito."
Hotunan jama'ar Anambra suna tururuwar karbar katikan zabensu kafin Asabar
A baya mun kawo cewa masu son kada kuri'a wadanda suka yi rijistar katin zabe a hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, da ke karamar hukumar Dunukofia a jihar Anambra sun bazama karbar katikan zabensu.
Daily Trust ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis, farfafjiyar ofishin hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta cika dankam da jama'a masu son karbar katikansu.
Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ya dinga amsa gaishe-gaishe da jama'ar da suka je karbar katikan zabensu.
Asali: Legit.ng