Hotunan jama'ar Anambra suna tururuwar karbar katikan zabensu kafin Asabar

Hotunan jama'ar Anambra suna tururuwar karbar katikan zabensu kafin Asabar

  • Jama'a sun dinga tururuwa tare da cika a ofishin hukumar zabe da ke Dunukofia a jihar Anambra
  • A ranar Alhamis, farfajiyar ofishin INEC ta cika da masu karbar katikan zabensu kafin zuwan ranar zaben
  • Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya fito da kanshi inda ya dinga gaishe-gaishe da jama'a

Anambra - Masu son kada kuri'a wadanda suka yi rijistar katin zabe a hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, da ke karamar hukumar Dunukofia a jihar Anambra sun bazama karbar katikan zabensu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis, farfafjiyar ofishin hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta cika dankam da jama'a masu son karbar katikansu.

Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ya dinga amsa gaishe-gaishe da jama'ar da suka je karbar katikan zabensu.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ƙungiyar IPOB ta saduda, ta soke dokar zaman gida na dole, ta ce a fita a yi zaɓe a Anambra

Ga hotunan da Daily Trust ta wallafa:

Hotunan jama'ar Anambra suna tururuwar karbar katikan zabensu kafin Asabar
Hotunan jama'ar Anambra suna tururuwar karbar katikan zabensu kafin Asabar. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel