Gwamna ya bayyana shirin PDP, ya ce ta shirya ceto Najeriya daga mummunan shugabanci
- Bayan taron gangamin da aka yi a Abuja cikin nasara, jiga-jigan jam’iyyar PDP sun tabbatar da cewa gari ya waye a Najeriya
- Gwamna Ifeanyi Okowa na daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar da ke bayyana kwarin gwiwar cewa sauyi na zuwa nan kusa
- Gwamnan na jihar Delta ya bayyana cewa a yanzu babbar jam’iyyar adawa ta shirya tsaf domin ceto ‘yan Najeriya daga mummunan shugabanci
Asaba - Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya bayyana cewa, nasarar gudanar da taron gangamin jam’iyyar PDP na kasa ya nuna yadda jam’iyyar ke shirin ceto Najeriya daga halin da ake ciki na rashin shugabancin da ya mamaye kasar.
Okowa ya bayyana hakan ne a yayin da yake magana a shirin gidan talabijin na Channels na "Politics Today" a ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba wanda Legit.ng ta sa ido a kai.
Ya ce ‘yan Najeriya sun gaji da tabarbarewar rashin tsaro da na tattalin arziki da ke addabar kasar, inda ya ce PDP ta samu nasarar gudanar da taronta, inda ya aike da sakon da ya dace ga ‘yan Najeriya cewa ya yi daidai da yadda za a canza munanan labari na mulkin APC.
A kalamansa:
“Muna bukatar mu sake haifar da fata; muna bukatar mu sa su yarda cewa Najeriya daya ce, Najeriya kasa ce dunkulalliya, kuma akwai fata ga sabuwar Najeriya.
"Tare da nasarar gudanar da taron gangaminmu na kasa, mun aika da sako tare da gamsuwa ga 'yan Najeriya cewa da gaske PDP a shirye take ta kubutar da su."
Bayan lashe zabe, sabon shugaban PDP ya mika zazzafan sako ga jam'iyyar APC
A baya kadan, Sabon zababben shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya aike da sako ga jam'iyyar APC mai mulki, yana mai cewa “zamu karbe kasar nan.”
Da yake magana da sanyin safiyar Lahadi bayan zaben sa a taron gangamin jam’iyyar na kasa a Abuja, Ayu ya bayyana shirin jam'iyyar na karbe mulkin kasar a zaben 2023, This Day ta ruwaito.
A cewarsa: “Nan da makonni biyu za ku ga karfin da zai dawo PDP a kowace jiha. Wasu tsirarun mutane sun yanke shawarar raba Najeriya. Za mu hada kan kasar don ci gaban kasar nan.
Asali: Legit.ng