A dage zaben gwamnan Anambra domin kare rayuka – Babban fasto ga FG
- Shahararren faston nan na Najeriya, Bishop Abraham Udeh ya yi kira ga dakatar da zaben gwamnan Anambra yan kwanaki kafin zaben
- Malamin addinin ya ce idan har aka yi zaben, toh za a yi zubar jini sosai a yawancin yankunan jihar
- Ya bayar da shawarar kara watanni shida domin gudanar da zaben
Anambra - Yan kwanaki kafin zaben gwamnan Anambra, shahararren faston nan na Najeriya, Bishop Abraham Udeh, ya ce ya zama dole hukumomin da abun ya shafa su gaggauta dakatar da zaben na ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba domin kare rayuka.
Bishop Udeh wanda aka fi sani da Fire By Fire ya ce ya ga jini na zuba tamkar kogi a jihar inda ake ta kururuwa da kuka a yankunan Anambra da dama.
Ya dage cewa mafita kwaya daya shine a kara watanni shida kafin ayi zaben, jaridar The Sun ta rahoto.
Ya bayyana cewa a tsakanin wannan lokacin ya zama dole a saki shugaban kujgiyar yan aware ta IPOB, Mazi Nnamdi Kanu sannan a aika shi Birtaniya domin samar da zaman lafiya a Kudu maso gabas da Najeriya gaba daya.
Ya ce:
“Yanayin ya sa dole na nemi a dakatar da zaben da dage shi zuwa sabon shekara. Kabilar Igbo na fuskantar rushewa. A saki Kanu ba tare da sharadi ba sannan a mayar da shi Turai.
“Akwai ajandar karar da matasan Igbo a sunan samar da tsaro don zaben Anambra.
“Ina shawartan Ohaneze Ndigbo da dukka shugabannin Igbo su dage kan dakatar da shi sannan majalisar dokokin jihar Anambra ta yi abun da ya kamata don dakatar da zaben. Za a zub da jini sosai, sai dai idan Allah ya sauya abun.”
Bishop Udeh ya bayyana cewa gwamnonin kudu maso gabas masu ci ba lallai ne su goyi bayan dakatar da zaben ba saboda muradinsu na son Shugaban kasa dan Igbo “wanda ba za a taba cimma ba.”
Rahoton ya kuma nuna cewa Faston ya bayyana cewa ta’addanci ya zama ruwan dare sannan ya yi danasanin cewa yan IPOB da yan bangansu kadai aka kira da yan ta’adda yayin da ba a kallon yan fashin daji da Fulani makiyaya masu makami da haka.
Ya kara da cewa:
“Wannan ita ce damar da suke ta nema da dadewa. Ku duba abun da ya faru a Izombe, jihar Imo.
“Ohaneze ta fito ta nema wa yan Igbo yanci. Ya zama dole Ohaneze ta fahimci cewa babu ta yadda Za a yi a bari dan Igbo ya zama shugaban kasar Najeriya, ba zai taba yiwuwa ba.
“Matakin kotu da arewa ta dauka don a bari Igbo su tafi abun dariya ne. Shin ba makirci bane na wahalar da fafutukar neman shugaban kasa na Igbo. Mun san duk wadannan abubuwan kuma wannan ne yasa dole Ohaneze ta nema wa Igbo yanci.
“An ce wani Shetima, dan Kungiyar arewa yana ta yi wa Ndigbo ba’a cewa tunda basu musulunta ba toh ba za a taba bari su samar da shugaban kasa ba.
“Toh Ina so na fada masa cewa kaso 90 cikin dari na yan Igbo basa ra’ayin mulkin mallaka. Muna bukatar jumhuriyyar kasar Igbo.”
Malamin ya ce ya yi tuni kan abun da ya faru a lokacin mulkin soji na farko a Najeriya lokacin da acewarsa, makiyan Igbo suka kashe shugaban kasa na mulkin soji na farko, Janar Johnson Umunnakwe Agui Ironsi.
Nnamdi Kanu ya fi zaben Anambra muhimmanci, ku sake shi don a samu zaman lafiya, Doyin Okupe
A gefe guda, tsohon hadimin tsohon shugaban kasar Najeriya, Dr Doyin Okupe ya bukaci gwamnatin tarayya ta saki shugaban IPOB don a samu zaman lafiya a kudu maso gabas bisa ruwayar The Punch.
Okupe ya koka a kan yadda gwamnati duk da ganin zubar da jinin da ke aukuwa a jihar amma za ta nuna halin ko-in-kula ta yi zabe a ranar 6 ga watan Nuwamba a jihar.
Ya ce akwai hatsari mai yawan gaske tattare da zaben da za a yi matsawar ba a saki Kanu ba, kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Asali: Legit.ng