Fadin gaskiya ne ya jawo ake hantarar Shugaban Majalisar Dokokin Filato - Dan majalisa

Fadin gaskiya ne ya jawo ake hantarar Shugaban Majalisar Dokokin Filato - Dan majalisa

  • Dan majalisa mai wakiltan Jos ta gabas/ta kudu a majalisar dokokin tarayya, Dachung Bagos, ya yi martani a kan tsige Ayuba Abok da aka yi a matsayin kakakin majalisar jihar
  • Bagos ya yi zargin cewa ana hantarar Abok ne saboda kawai yana fadin gaskiya kan halin da tsaro ke ciki a jihar
  • Ya kuma bayyana tsigewar a matsayin juyin mulki wanda ya saba wa kundin tsarin mulki

Filato - Dan majalisa mai wakiltan mazabar Jos ta gabas/Jos ta kudu a majalisar dokokin tarayya, Dachung Bagos, ya yi zargin cewa ana hantarar tsigaggen kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Ayuba Abok ne saboda fadar gaskiya.

Bagos ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan tsige shi, 'yan sanda sun kame shugaban majalisar dokokin Filato da tawagarsa

Fadin gaskiya ne ya jawo ake hantarar Shugaban Majalisar Dokokin Filato - Dan majalisa
Fadin gaskiya ne ya jawo ake hantarar Shugaban Majalisar Dokokin Filato - Dan majalisa Hoto: Fabulousmanji Cishak
Asali: Facebook

Ya ce an tsige kakakin majalisar ba bisa ka'ida ba domin shida daga cikin mambobin majalisar 24 ne suka aikata hakan, wanda a cewarsa ya yi kasa da kaso 2/3 da kundin tsarin mulki ke bukata don tsigewa.

Rahoton ya kuma ce Bagos ya kara da cewa an tsige kakakin majalisar ne ta karfi da yaji saboda ya fadi gaskiya a kan halin da tsaro ke ciki a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"A matsayina na wakilin mutane daga jihart Filato, mai wakiltan mazabar Jos ta kudu, Jos ta gabas, kuma a kan wani muhimmin batu da ke ci wa mazabata tuwo a kwarya.
“Dan mazabar tawa, wanda shine kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Honourabe Ayuba Abok, wanda shine halastaccen kakakin majalisar dokokin jihar Filato tun kafa majalisar a 2019.
"Saboda jajircewarsa a kan mutanensa sakamakon kashe-kashe da rashin tsaro a jihar, fadar magana yadda yake, bayyana gaskiyar al'amari yadda yake faruwa a Filato sakamakon rashin tsaro da kuma kokarin samar da mafita mai dorewa, a matsayinsa na kakakin majalisa, ya sa a yanzu ake hantararsa, saboda fadin gaskiya.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Sabuwar dirama ya yin da fusatattun matasa suka mamaye majalisar dokokin jihar Filato

"Abun takaici ne, cewa yan kwanakin da suka gabata, an aiwatar da juyin mulki a majalisar dokokin jihar Filato. Cewa, yan majalisa su shida suka aiwatar da juyin mulki ta hanyar tsige kakakin majalisar.
"Ya zama dole mutum ya damu. Ba wai don ya kasance dan mazabata ba, illa a matsayin mai kare kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya, inda sashe na 92 ​​karamin sashe na 2 ya bayyana karara cewa, kashi biyu cikin uku na 'yan majalisar jiha ne za su iya tsige kakakin majalisa.
"Amma sai ga shi, a majalisar dokokin Filato, muna da 'yan majalisa 24 da aka zaba. Sannan sai mutum shida suka zauna sannan suka aiwatar da juyin mulki da sunan tsigewa. Cewa, an tsige kakakin majalisa.
"Shida daga cikin 24, wanda karara ya saba wa kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya, sashi na 92, ta yadda mambobi shida ba za su taba zama kaso biyu cikin uku na 24 ba."

Kara karanta wannan

Ba ni da hannu a dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a gidan Mary Odili, Malami

Bayan tsige shi, 'yan sanda sun kame shugaban majalisar dokokin Filato da tawagarsa

A gefe guda, mun kawo cewa rikicin da aka yi a majalisar dokokin Filato ya dauki wani yanayi mai ban tsoro a ranar Litinin yayin da jami’an tsaro suka kame tsigaggen kakakin majalisar dokokin jihar, Abok Ayuba da wasu ‘yan majalisa 10 da ke masa biyayya.

Da misalin karfe 3:15 na rana, kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, Edward Ebuka, ya tasa ‘yan tawagar tsohon kakakin majalisar su 11 a motocin Hilux guda hudu, The Nation ta ruwaito.

Idan baku manta ba, a ranar Alhamis din da ta gabata ne wasu 'yan majalisu a jihar suka tsige shugaban majalisar, lamarin ya jawo cece-kuce da gardama, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng