Ana neman tsigaggen kakakin majalisar Plateau ruwa a jallo

Ana neman tsigaggen kakakin majalisar Plateau ruwa a jallo

  • Kakakin majalisar jihar Plateau, Yakubu, ya ayyana neman abokin aikinsa Abok Ayuba ruwa a jallo
  • Hakan na zuwa ne bayan Ayuba ya yi yunkurin zama shugaban kakakin majalisar Plateau amma hakan bai yi wu ba
  • Kazalika, Yakubu ya kuma dakatar da wasu yan majalisun jihar guda biyar da suke goyon bayan Ayuba

Jihar Plateau - Rikicin da ya barke a majalisar dokokin jihar Plateau ya dau sabon salo bayan an ayyana neman tsigaggen kakakin majalisar, Abok Ayuba, ruwa a jallo.

An yi fito na fito a majalisar a ranar Litinin tsakanin magoya bayan yan majalisar biyu, dukkansu yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a yayin da suke kokarin karbe iko a majalisar.

Har sai da yan sanda suka iso harabar majalisar sannan suka kwantar da tarzomar.

Ana neman tsigaggen kakakin majalisar Plateau ruwa a jallo
Majalisar Dokokin Jihar Plateau. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Bayan tsige kakakin majalisar, ya fita zuwa wani wurin taro inda ya yi zaman majalisar ya kuma sanar da dakatar da yan majalisa shida da suka jagoranci tsige shi.

Kara karanta wannan

Bayan tsige shi, 'yan sanda sun kame shugaban majalisar dokokin Filato da tawagarsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tun lokacin, Ayuba da Yakubu, kowannensu na ikirarin shine kakakin majalisar na ainihi.

Daily Trust ta rahoto cewa Ayuba da yan majalisa masu goyon bayansa sun sulale sun shiga majalisar misalin karfe 4 na asuba a ranar Litinin, sai dai bayan yan mintuna, Yakubu abokin hamayyarsa shima ya taho da mutanensa.

An ruwaito cewa bangarorin biyu sun shiga taro inda Ayuba ya yi ta jadada cewa yana son a mayar da shi matsayinsa na kakakin majalisa.

Wata majiya ta ce:

"Ayuba ya bukaci a mayar da shi a matsayin kakakin majalisa daga baya zai yi murabusa sannan ya kyalle Yakubu ya zama kakakin majalisa, amma yan majalisa magoya bayan Yakubu ba su amince ba."

Daily Trust ta ruwaito cewa jim kadan bayan hakan, Yakubu ya ayyana neman Ayuba ruwa a jallo bayan ya jagoranci zaman majalisar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Zanga-Zangar Matasa a majalisar dokoki ta dauki sabon salo, An fara harbe-harbe

Ba bu tabbas ko yana da ikon ayyana neman abokinsa dan majalisa ruwa a jallo.

Ya sanar da dakatar da yan majalisa shida masu biyayya ga tsigaggen kakakin majalisar.

Yan majalisar sun hada da:

  • Henry Longs (Pankshin South)
  • Dangtong Timothy (Riyom)
  • Musa Agah (Rukuba/Iregwe)
  • Bala Fwanje (Mangy South) da
  • Nambol Listic (Langtang North)

Kakakin majalisar ya ce an dakatar da su saboda zaman da suka yi a dakin taro a ranar Alhamis da kutse cikin harabar majalisar a jiya.

Ya ce:

"Don haka, muna ayyana neman (tsigagen kakakin) ruwa a jallo saboda aikata abubuwa da suka saba wa dokokin majalisa."

Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro su kama Ayuba saboda yawo da sandan ikon majalisa na bogi.

Dan takarar gwamna ya sharɓi kuka a bainar jama'a yayin yaƙin neman zaɓe a Anambra

A wani rahoton, dan takarar gwamna na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba, Dr Obiora Okonkwo, ya zubar da hawaye a yayin da ya ziyarci garin Okpoko don kaddamar da aikin titi na miliyoyin naira a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Sabuwar dirama ya yin da fusatattun matasa suka mamaye majalisar dokokin jihar Filato

Aikin titin zai fara ne daga Ede Road, School Road/Awalite da Ojo street ya tsaya a Owerri road a garin Okpoko a karamar hukumar Ogbaru a jihar ta Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

Okonkwo ya zubar da hawaye ne a lokacin da ya ga wata mata mai shayarwa mai shekaru 30 wadda ta fada cikin kwata bayan ta kasa bin titin saboda rashin kyawunsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164