Cikin hotuna: Matashi mai shekaru 25 da ya lashe kujerar shugaban matasan PDP
- Wakilan jam'iyyar PDP ta zabi matashi mai jini a jika a matsayin shugaban matasan jam'iyyar
- Rahoto ya bayyana cewa, matashin mai shekaru 25 ya doke mutane uku, inda ya yi nasara a kansu
- A karon farko, jam'iyyar PDP ta samar da shugaban matasan jam'iyyar wanda shi ne mafi kankanta
Abuja - Rahotanni da muke samu daga jaridar Punch sun bayyana cewa, wani dan shekara 25 ne ya zama shugaban matasan jam'iyyar PDP na kasa.
An zabi Mohammad Kadade Suleiman mai shekaru 25 a matsayin shugaban matasan jam'iyyar PDP na kasa. An zabe shi ne a babban taron jam’iyyar na kasa da aka kammala a Abuja.
A jiya Asabar ne aka gudunar da taron gangamin PDP, taron da ya sami halartar jiga-jigan jam'iyyar ta PDP daga sassa daban-daban na kasar nan.
Daga cikin jadawalin taron gangamin, an gudunar zaben shugabannin jam'iyya, inda aka sanar da waye sabon shugaban PDP da wasu 20 da suka lashe kujerun shugabancin.
Daga cikinsu, akwai Mohammad Kadade Suleiman, wanda aka kadawa kuri'u mafi yawa a rukunin shugabancin matasan jam'iyyar PDP.
Jaridar This Day ta ruwaito cewa, Kadade ya samu kuri'u 3072, inda ya doke 'yan takara uku masu neman kujerar.
Kalli hotunan sabon shugaban matasan jam'iyyar PDP
PDP ta hango karshen jam'iyya mai mulki ta APC, inji Sanata
A wani labarin, Shugaban kwamitin karramawa na taron gangamin jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Ifeanyi Okowa, a ranar Juma’a, 29 ga watan Oktoba, ya ce tsare-tsare da sakamakon atisayen zai tabbatar da cewa jam’iyyar a shirye take ta ceto Najeriya daga kalubalen da ke addabarta.
Okowa, wanda shine gwamnan jihar Delta ya bayyana haka ne a jawabinsa a taron kwamitin da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar ta kasa a Abuja.
Ya ce jam’iyyar PDP a shirye take ta karbi ragamar shugabancin kasar a shekarar 2023, yana mai jaddada cewa taron zai karfafa hadin kai da dimokradiyya ba a jam’iyyar kadai ba har ma a kasar baki daya.
Asali: Legit.ng