Dan wani Sarki a Arewa ya shiga jam'iyyar adawa, ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023
- Ɗan Sarkin Ebiraland kuma sanannen ɗan kasuwa, Yarima Malik, ya shiga jam'iyyar ɓangaren hamayya ta matasa YPP
- Yariman ya kuma bayyana shirinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen dake tafe na shekarar 2023
- A cewarsa lokaci ya yi da matasa zasu fito su nemi yancin su, domin bai kamata su zuba ido komai na kasa ya lalace ba
Kogi - Ɗaya daga cikin ƴaƴan Basaraken Ebiraland kuma ɗan kasuwa, Yarima Malik Ado-Ibrahim, ya shiga jam'iyyar Young Progressives Party (YPP).
Leadership ta ruwaito cewa Yariman ya bayyana sha'awarsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023 dake tafe.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, Ado-Ibrahim yace ya ɗauki matakin tsayawa takara ne saboda ya fahimci akwai rashin kwarewa a jagorancin ƙasar nan.
Yace Najeriya tana bukatar shugaba wanda zai haɗa kan kowa, wanda zai jawo kowa a jikinsa ba tare da duba yarensa, ko addininsa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa yariman zai nemi kujera lamba ɗaya?
Vanguard ta rahoto a jawabinsa, yarima Ado Ibrahim yace:
"Wannan lokaci ne na daban a Najeriya, mun ga zamani na musamman, mutane na cire rai da gyaruwar Najeriya. Muna da kwarewa a tare da mu amma mun tsaya komai na ƙara taɓarɓarewa."
"Abin da ka shuka shi zaka girba, kada mu yi tsammanin mun bar komai ya lalace kuma muce zamu cigaba."
"Ina son ƙasata Najeriya, na yi rayuwata a ƙasashen waje na tsawon shekara 47, na nemi ilimi, na yi aiki tuƙuru , kuma na dawo gida."
Meyasa ya shiga jam'iyyar YPP?
Game da dalilinsa na zaɓar jam'iyyar YPP, yace:
"Na shiga jam'iyyar YPP ne saboda duk jam'iyyar siyasan da na shiga a ƙasar nan watsar da ni za'ayi can ƙasa."
"Ina kira ga matasan ƙasar nan, kada su cire rai, wannan lokacin ku ne kada ku tsaya wata-wata akwai jam'iyyar dake bukatar ku mai suna YPP."
A wani labarin kuma Saraki ya yi magana kan kudirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 da shirin sauya sheka daga PDP
Tsohon shuagaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, yace a wurinsa baya kallon siyasa a bukatun karan kansa kaɗai.
Dailytrust tace Saraki ya faɗi haka ne yayin da yake bada amsa kan ko zai fice daga PDP matuƙar ba ta bashi tikitin tsayawa takarar shugaban ƙasa ba a 2023.
Asali: Legit.ng