Yadda yan majalisun PDP da APC suka fafata wajen tsige shugaban majalisar dokokin Filato
- Majalisar dokokin jihar Filato ta tsige shugaban majalisar, Honorabul Abok Ayuba Nuhu
- Rahotanni sun bayyana cewa mambobin majalisar 16 cikin 24 ne suka kaɗa kuri'ar tsige kakakin majalisan
- Bayan tunɓuke shi, majalisar ta kuma amince da maye gurbinsa da Honorabul Sanda Yakubu
Plateau - Majalisar dokokin jihar Filao ta tsige kakakinta, Honorabul Abok Ayuba Nuhu, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Rahoto ya bayyana cewa an maye tsohon kakakin da Honorabul Sanda Yakubu, wanda ya fito daga mazabar Pingana, karamar hukumar Bassa, jihar Filato.
Mambobin majalisa 16 cikin 24 na majalisar dokokin ne suka kada kuri'ar amince wa da tsige shugaban nasu a zaman majalisa na yau Alhamis.
Channels TV ta rahoto cewa Mambobin majalisa na jam'iyyar APC mai mulki ne suka tsige shugaban da sanyin safiyar Alhamis.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Legit.ng Hausa ta gano cewa an tsaurara matakan tsaro a hanyar shiga majalisar, domin sai da jami'an tsaro suka raka mambobin zuwa cikin zauren.
Hotunan yadda aka tsaurara tsaro
Yadda lamarin ya faru
Tun da misalin ƙarfe 5:30 mambobin majalisar harda na jam'iyyar hamayya suka mamaye zauren majalisar.
An yi musayar yawu tsakanin ɓangarorin biyu na PDP da APC yayin da aka gabatar da kudirin tsige kakakin majlisar.
Mambobin jam'iyyar adawa PDP, waɗanda ke nuna goyon bayansu ga shugaban majalisar, sun yi kokarin hana tsige shi ta hanyar ɗauke sandar majalisa.
Amma mambobin APC, waɗanda suke da mafi rinjaye a majalisar, sun kwace sandar tare da maida ta inda take, kuma aka cigaba da bin matakan tsigewan.
Meyasa aka tsige shi?
Rahotanni sun bayyana cewa na fara takun saka tsakanin kakakin majalisa da kuma Gwamnan jihar, Simon Lalong, bayan harin Yelwan Zagam.
2023: Kura Ta Kara Turnuke Wa Atiku, Shugabannin PDP a Wata Jiha Sun Yi Fatali da Sunayen Tawagar Kamfe
Bayan kai harin, kakakin majalisar ya fara sukar gwamna a bayyane, kuma ya daina halartar ayyukan gwamnatin jihar.
A wani labarin kuma Saraki ya yi magana kan kudirin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 da shirin sauya sheka daga PDP
Tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Abubakar Bukola Saraki, yace yanzun ba ya tunanin kansa a siyasar Najeriya.
Saraki yace a halin yanzun fatan sa shine PDP ta shawo kan matsalolinta, ta zama tsintsiya ɗaya domin ceto Najeriya daga hannun APC.
Asali: Legit.ng