Ba mu damu da rikicin dake faruwa ba saboda mun san Allah yana tare da mu, Gwamnan PDP

Ba mu damu da rikicin dake faruwa ba saboda mun san Allah yana tare da mu, Gwamnan PDP

  • Babbar jam'iyyar adawa a ƙasar nan, PDP, tace tana aiki ba ji ba gani wajen shawo kan rikicin cikin gida da ya addabe ta kafin babban taro
  • Gwamnan jihar Delta, kuma shugaban kwamitin tantancewa, Ifeanyi Okowa, yace PDP ba ta damu da abubuwan dake faruwa ba
  • A cewar gwamnan, PDP na da ƙarfin guiwar shawo kan matsalolinta kuma zata samu nasara a babban gangaminta dake tafe

Abuja - Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa tana aiki ba ji babu gani domin warware matsalolin cikin gida da ya addabe ta yayin da babban gangaminta da yake ƙaratowa ranar Asabar.

Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, kuma shugaban kwamitin tantacewa na jam'iyyar PDP, shine ya bayyana haka a sakateriyar PDP ta ƙasa dake Abuja ranar Talata.

The Cable ta rahoto gwamnan na cewa PDP ba ta damu da rikicin dake faruwa ba domin tana da kwarin guiwar warware matsalolin a cikin gida.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

Gwamna Okowa
Ba mu damu da rikicin dake faruwa ba saboda mun san Allah yana tare da mu, Gwamnan PDP Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Okowa yace:

"Muna kokarin magance abinda ke faruwa, wanda ya haɗa da kokarin hana gangamin taron mu a kotu, kuma mun yi nisa sosai."
"Muna da yaƙinin shawo kan lamarin, zuwa ranar Alhamis zamu gama tantance adadin wakilan mu. Zan faɗa muku adadinsu ranar Jumu'a da safe."

Allah na tare da mu - Gwamna Okowa

Gwamnan ya kuma ƙara da cewa jam'iyyarsa ta PDP ba ta damu da abun dake faruwa ba domin tasan zata shawo kansu ba da jimawa ba.

"Bamu damu ba saboda zamu iya shawo kan matsalolin kuma Allah yana tare da mu. Idan ka duba mafi yawan yan takara ba su da abokan fafatawa."
"Wannan alama ce dake nuna PDP na kan hanyar samun nasara a taronta. Ba mu fatan samun matsala daga wakilan mu, amma idan muka samu umarnin kotu, to bamu da wani zaɓi da ya wuce mu cire su."

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

"Mun fahimci cewa matukar bamu sami matsala a wurin tantancewa ba to ba zamu samu matsala a gangamin mu ba, bama fatan samun matsala."

A wani labarin kuma mun kawo muku cewa wata yar majalisar dokoki ta jam'iyyar PDP ta rigamu gidan gaskiya bayan fama da rashin lafiya

Honorabul Ironbar ta mutu ne ranar Talata 26 ga watan Oktoba, kuma itace yar majalisa ta biyu da ta mutu a majlisa ta 9.

Kafin rasuwarta, marigayya ta kasance mamba a jam'iyyar hamayya PDP kuma ta ɗare kan mulki tun shekarar 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262