2023: Saraki ya bayyana yadda PDP za ta yi da tikitinta na shugaban kasa

2023: Saraki ya bayyana yadda PDP za ta yi da tikitinta na shugaban kasa

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya yi martani a kan yankin da jam'iyyar PDP za ta bai wa tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2023
  • Saraki ya bayyana cewa babbar jam'iyyar adawar kasar ta rungumi tsarin bude takarar tikitin ga dukkan yan takarar da ke muradi daga kowani yanki na kasar
  • Ya ce burinsu kawai shine a samu dan takara mafi cancanta da zai kwato kasar daga hannun APC a zabe mai zuwa

Abuja - Gabannin babban zaben 2023, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki, ya yi tsokaci a kan tsarin da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za ta bi wajen zabar dan takarar shugaban kasa.

Saraki ya ce duk da cewar PDP ta mika tikitin ciyaman dinta na kasa ga yankin arewa ta tsakiya, bata da niyar hana kowani dan takara daga kowani yanki neman shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

Atiku zai iya gyara Najeriya: Gwamna ya bayyana gogewar Atiku da PDP a iya mulki

2023: Saraki ya bayyana yadda PDP za ta yi da tikitin shugaban kasa
2023: Saraki ya bayyana yadda PDP za ta yi da tikitin shugaban kasa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Jaridar Sun ta rahoto cewa Saraki ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da Arise TV ta yi da shi ranar Talata, 26 ga watan Oktoba.

Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya yi watsi da rade-radin cewa jam'iyyar za ta mika tikitinta na shugaban kasa ga yankin kudu tunda ta bai wa arewa tikitin ciyaman na kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce shugabancin jam'iyyar ta jadadda jajircewarta na bude takarar tikitin shugaban kasa ga dukkanin yankunan kasar idan har hakan zai sa ta samu dan takara mafi cancanta daga tsarin, rahoton The eagle.

Ya ce:

"Kan batun shiyya, jam'iyyar ta bayyana karara a dukkan tarukanmu cewa koda dai mun raba mukaman jam'iyyar, ba za ta hana duk mai muradin takarar shugaban kasa tsayawa ba.
"Yawancin shugabanninmu sun bayyana hakan, kuma mun bayyana hakan a taronmu na NEC, da kuma dukkan taruka, cewa koda dai mun kai kujerar ciyaman din jam'iyyar na kasa yankin arewa ta tsakiya, hakan ba zai hana kowa yin takara ba.

Kara karanta wannan

2023: Mawakin Buhari, Rarara ya yanke shawarar tsayawa takarar majalisar tarayya

"Abun da muke nema shine dan takara mafi cancanta da zai lashe zaben."

Saraki: Kwanan nan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC za su sauya sheka zuwa PDP

A gefe guda, mun ji a baya cewa, Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya ce kwanan nan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC za su sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.

Tsohon gwamnan jihar Kwara ya bayyana cewa dama PDP ba ta girgiza ba da sauya shekar da wasu gwamnonin PDP su ka yi zuwa APC, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Gwamnoni kamar Ben Ayade na Cross River, Dave Umahi na jihar Ebonyi da Bello Matawalle na jihar Zamfara sun koma jam’iyya mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng