Siyasar Kano: Kwankwaso ya bayyana ra'ayinsa kan tafiya da Shekaru a siyasa
- Yayin da ake ci gaba da hango rikici tsakanin Kwankwaso da Shekarau, Kwankwaso ya bayyana wata magana
- A cewarsa, zai iya zama a inuwar siyasa daya da Malam Shekarau idan Allah ya nufi hakan
- Ya kuma bayyana irin alherin da ya yi wa gwamna Ganduje na jihar Kano a shekarun baya
Kano - Daily Trust ta rahoto cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da Sanatan da ke wakiltar Kano ta Tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau, kafin shekarar 2023.
Ya kuma ce bai yi mamakin wutar rikicin da ke ruruwa a jam'iyyar APC mai mulki a Kano tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da sanatan ba.
Da yake magana a wata hira da BBC Hausa, jigon na Jam’iyyar PDP ya ce:
“Duk wanda ba zai iya rama abubuwan alherin da aka yi masa tsawon shekaru ba, saboda shi da kansa (Ganduje) ya ambata cewa mun yi mashi kaza da kaza. Kuma mutane da yawa sun ji haka.
“Amma lokacin da ya hau karagar mulki, ya gaza yi wa Kwankwaso da mabiya Kwankwasiyya alheri. To ta yaya kuke tsammanin zaman lafiya zai kasance? Na san yana zuwa, lokaci ne kawai"
Da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa Shekarau ya yaba masa, Kwankwaso ya ce ya ji dadin kalaman.
Dangane da ko za su ci gaba da zama a inuwar siyasa daya, Kwankwaso ya ce ba zai yi mamaki ba domin idan Allah ya kaddara hakan ta faru, za ta faru, ya kara da cewa idan ba haka ba, za su ci gaba da gode wa Allah Madaukakin Sarki.
Tsohon ministan ya bayyana cewa ya yi shiru a PDP ne saboda rashin adalcin da aka yi wajen zaben shugabanni a reshen Kaduna na jam'iyyar.
Ya ce bayan sun gudanar da zaben, wasu daga cikin shugabanni masu son kai sun yanke shawarar haifar da matsaloli ga shugabancin Kano, wanda a cewarsa, yanzu an warware su.
Amma, ya ce ya ci gaba da kasancewa dan PDP.
Idan baku manta ba, Shekarau ya gaji Kwankwaso a matsayin sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya.
Sabbin bayanai kan shirin tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Kwankwaso, na sauya sheka zuwa APC
A wnai labarin, Rahotanni sun bayyana wasu dalilai da yasa har zuwa yanzun tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, bai koma APC ba gabanin 2023.
Majiya mai ƙarfi ta shaidawa Leadership cewa Kwankwaso na fatan tsira da mutuncinsa kuma ya kafa wa APC wasu sharuɗɗa na shiga jam'iyyar.
Kasancewar ana ta cece-kuce kuma shugabannin Arewa na ganin ya kamata a baiwa kudu takarar shugaban ƙasa a 2023, Kwankwaso ya kafawa APC sharaɗin cewa za'a ba shi kujerar mataimaki a 2023.
Asali: Legit.ng