2023: Sai mun tabbatar Tinubu ya zama shugaban ƙasan Najeriya, Adewale
- Jiga-jigan jam’iyyar APC na jihar Legas sun lashi takobin ganin sun cika wa Asiwaju Bola Tinubu burin sa
- Sakataren jam’iyyar na reshen jihar Legas, Comrade Ayodele Adele ya ce za su tabbatar Tinubu ya zama shugaban kasa
- A cewarsa, ya jajirce wurin yin aiki tare da shugaban jam’iyyar na jihar Legas, Hon. Cornelius Ojelabi don ganin hakan ta tabbata
Jihar Legas - Masu fada a ji na jam’iyya mai mulki, APC na reshen jihar Legas sun lashi takobin ganin Asiwaju Bola Tinubu ya zama shugaban kasar Najeriya a 2023.
A wata tattaunawa da Vanguard ta yi da sakataren jam’iyyar na jihar Legas, Comrade Ayodele Adewale ya tabbatar da cewa shugabannin APC karkashin Cornelius Ojelabi za su tabbatar Tinubu ya zama shugaban kasa.
Tsohon shugaban karamar hukumar Odofin, Adewale ya yi godiya ga shugabannin jam’iyya akan yin amanna da shi inda ya ce:
“Na jajirce wurin yin aiki tare da Hon. Cornelius Ojelabi a matsayin sa na shugaban APC a jihar Legas."
Ya ce za su yi kokarin ganin sun samu nasara mai yawa ga jam’iyyar su , jihar Legas da kasar Najeriya gabadaya.
Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, ya bayyana cewa:
“Za mu yi aiki tukuru don tabbatar da ganin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban kasan Najeriya a ranar 29 ga watan Mayun 2023.”
Da Duminsa: A karon farko, Shekarau ya fita rangadi da sabon shugaban APC na tsaginsu a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa an gano tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, a ranar Talata, a wurin taro tare da Ahmadu Haruna Zago, shugaban jam'iyyar APC na tsagi guda a jihar Kano.
Shugabancin kasa a 2023: Tinubu na kara samun goyon baya, ya gana da tsohon shugaban majalisar dattawa
An gan su ne a wurin taron bawa al'umma tallafi da Shekarau, Sanata mai wakiltan Kano ta tsakiya ya shirya.
Shirin tsarin tallafi ne na koyar da saka da bada kananan jari ga masu sana'o'i kan ilimin tsafta da amfaninsa a Kano Central da kewaye.
Asali: Legit.ng