Da Duminsa: Yan sanda sun fara bincike kan yadda jami'an tsaro suka kaɗa kuri'a a zaben APC na tsagin Ganduje
- Wasu hotunan bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda wani ƙaramin sufetan yan sanda ya kaɗa kuri'a a zaɓen APC na Kano
- Mataimakin sufetan yan sandan ƙasar nan mai kula da shiyya ta ɗaya, Abubakar Sani Bello, ya bada umarnin bincike
- Jam'iyyar APC ta faɗa rikici a jihar Kano, tun bayan da tsohon gwamnan jihar, Malam Shekarau, ya ja tawagarsa daban
Kano - Rundunar yan sandan ƙasar nan ta bada umarnin gudanar da bincike kan jami'in ɗan sandan da aka gani a hoton bidiyo yana ƙada kuri'a.
Dailytrust ta ruwaito cewa wani hoton bidiyo da ya watsu ya nuna wani ɗan sanda yana kaɗa kuri'a a wurin taron jam'iyyar APC na jihar Kano, wanda ya gudana ranar Asabar.
A bidiyon, an hangi jami'in a gefen Abdullahi Abbas, sabon zababben shugaban jami'iyyar APC na tsagin Gwamna Ganduje na jihar Kano.
A wata sanarwa da kakakin rundunar yan sanda na shiyya ta ɗaya, Abubakar Zayyanu, ya fitar, yace mataimakin sufetan yan sanda na ƙasa, Abubakar Sadiq Bello, ya bada umarnin bincike kan jami'in.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mataimakin sufetan ya kira lamarin da abun takaici kuma da rashin gogewar aiki, a cewar sanarwan, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Meyakai ɗan sandan ya kaɗa kuri'a?
Rahotanni sun bayyana cewa ɗan sandan mai suna, Bashir Muhammed, yana aiki ne a gidan gwamnatin Kano, daga nan ne aka haɗa shi aiki tare da shugaban APC na jihar.
Wani sashin sanarwan yace:
"An jawo hankalin hedkwatar yan sanda ta shiyya ta ɗaya, kan wasu hotunan bidiyo dake yawo na wani ɗan sanda yana ƙaɗa kuri'a zaɓen APC na jihar Kano, tare da wanda yake ba kariya, shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas."
"Ɗan sandan yana aiki ne a gidan gwamnatin jihar Kano, daga nan ne aka haɗa shi ya yi aiki tare da Abdullahi Abbas, wajen ba shi tsaro."
"AIG ya bada umarnin bincike, kuma da zaran an gano ɗan sandan yana da laifi, za'a ɗauki matakin da ya dace a a kan shi."
A wani labarin kuma Babban dalilin da yasa yan Najeriya ba zasu amince da Igbo a matsayin shugaban ƙasa ba
Ɗaya daga cikin jiga-jigan PDP, Raymond Dokpesi, yace ba dalilin da zaisa yan Najeriya su amincewa ɗan Igbo ya shugabance su.
Shugaban kamfanin DAAR yace kamata ya yi PDP ta sake baiwa Atiku Abubakar, daga yankin arewa maso gabas dama.
Asali: Legit.ng