Jerin matasan Najeriya 6 da suka hau kujerun gwamnoni, sun dauki tsauraran matakai
Saboda kokarinsu a makaranta, an ba wasu matasan ‘yan Najeriya damar da ba kowa ke samu ba domin jagorantar jihohi gaba daya a matsayin gwamna sannan aka karfafa masu gwiwar daukar muhimman matakai.
Koda dai dai an ba wadannan matasa damar zama gwamnonin jihohinsu na akalla kwana daya, karramawar ta taimaka wajen karfafa wannan maganar da ke cewa yara manyan gobe.
1. Atika Aminu Yankaba (Kano)
Domin bikin ranar yara mata ta duniya a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya mika gwamnatin jihar ga Yankaba na mintuna 20 kacal.
Bayan ta karbi mulki a matsayin Gwamnan jihar yan arewa, Yankaba ta gudanar da taron yan majalisar jiha sannan ta ba ilimin yara mata muhimmanci a ajandar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A taron, Gwamna Yankaba ta bayyana cewa akwai bukatar jihar ta ware karin kudi don gina karin makarantun gwamnati da kuma daukar kwararrun malamai.
2. Aisha Katagum (Bauchi)
Daga cikin bikin ranar yara mata ta duniya na 2021, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na jihar Bauchi a ranar Talata, 12 ga watan Oktoba, ya sauka daga kujerarsa don Aisha Katagum (mai shekaru 14) ta makarantar gwamnati, Katagum ta haye.
Bala ya yi bayanin cewa ya mika mulki ga Aisha da sauran yara matan da suka kasance yan majalisar jihar na wucin gadi a kokarinsa na karfafa masu gwiwar kara kaimi a harkokin karatunsu.
3. Nicholas Ogunji (Abia)
Wani matashi, Nicholas Ogunji, shima ya samu wannan dama a 2020 lokacin da Gwamna Okezie Ikpeazu ya bar masa kujerar na kwana daya.
Dalibin na makarantar Adventist Technical Secondary School Ogunji mai shekaru 17, wanda ya kasance namiji na farko da ya zama gwamnan jihar na kwana daya ya saki wasu fursunoni a gidan yarin Afaraukwu bayan ya biya masu tararsu.
4. Jemimah Marcus (Lagos)
A matsayin karramawa bayan lashe gasar iya kawo haruffan kalma a 2020, Jemimah Marcus, dalibar makarantar Angus Memorial Senior High School, ita ma ta samu damar zama gwamna ta kwana daya a jihar.
5. Chineme Joy Ota (Abia)
Wata marainiya mai kwazo a karatu, Chineme Joy Ota ta kasance daliba mai shekaru 18 a makarantar Ohafia Girls Model Secondary School mai a Abia lokacin da aka bata damar zama gwamna na kwana daya a jihar a 2018.
Da take zantawa da mambobin majalisarta mai mutum 20 a waccan lokacin, Gwamna Ota ta yi magana kan samar da cibiyar walwalar matasa a jihar domin magance lamuran cin zarafin kananan yara.
Gwamnar ta tuna cewa a matsayinta na marainiya a kankantar shekarunta, ta fuskanci cin zarafi.
6. Edun Olabanji (Lagos)
A mulkin tsohon gwamna Babatunde Fashola na Lagos, Edun Olabanji, dalibin makarantar sakandare na Sojoji mai shekaru 15 a waccan lokacin kuma dan kafinta, ya zama gwamna na kwana daya a jihar bayan ya lashe gasar iya karanto haruffan kalmomi a 2014.
2023: Osinbajo ya ja-kunnen matasan Najeriya, yace babu wanda zai ba su mulki a bagas
A wani labarin, Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi kira ga matasa su fito takara a zabe mai zuwa na 2023, idan har suna neman mulki.
Jaridar The Cable tace Yemi Osibajo ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi wani jawabi wajen wani taron da aka shirya wa ‘yan majalisa a garin Legas.
Da yake magana, Farfesa Osinbajo ya fada wa matasa babu wanda zai dauki mulki ya damka masu, yace shigar su siyasa ne zai kawo sabon jini a harkar.
Asali: Legit.ng