2023: Osinbajo ya ja-kunnen matasan Najeriya, yace babu wanda zai ba su mulki a bagas
- Farfesa Yemi Osinbajo yace dole matasa su tashi tsaye, su nemi mulki a 2023
- Mataimakin shugaban kasar yace babu wanda zai ba matasan mulki a araha
- Osinbajo ya bayyana haka yayin da Babajide Omoworare ya wakilce sa a taro
Lagos - Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi kira ga matasa su fito takara a zabe mai zuwa na 2023, idan har suna neman mulki.
Jaridar The Cable tace Yemi Osibajo ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi wani jawabi wajen wani taron da aka shirya wa ‘yan majalisa a garin Legas.
Da yake magana, Farfesa Osinbajo ya fada wa matasa babu wanda zai dauki mulki ya damka masu, yace shigar su siyasa ne zai kawo sabon jini a harkar.
Daily Trust tace mai taimaka wa shugaban kasa wajen harkokin majalisa (dattawa), Babajide Omoworare, ya wakilci mataimakin shugaban kasa a taron.
Jerin yan arewa da Tinubu zai iya dauka a matsayin abokan takara idan ya shiga tseren shugaban kasa na 2023
Osinbajo yake cewa idan har matasa ba su fito takara a zabe ba, fafutukar not-too-young-to-run da ake rika yi domin a ba matasa dama ta zama wahalar banza.
Babajide Omoworare ta bakin Farfesa Yemi Osibajo yake cewa gwamnati tana ta yi wa matasan Najeriya tanadi domin su zama shugabanni wata rana a kasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Osinbajo ya yi jawabi
“Domin a shirya wa babban zabe na 2023, dole matasa su fito sosai su tsaya takara, abin ka da ya zama surutu a baki kurum.”
“Ba a mika mulki a araha. Idan ba ka nema ba, ba za kayi nasara ba. Dole ne kuma muyi rajistan zabe.”
“Babban Makasudin shi ne a tabbatar da cewa matasa sun shiga harkar siyasa, kuma suna aikin majalisa.”
A karshe Osinbajo ya koka cewa matasa ba su fita zabe sosai a Najeriya, yace a sauraren wurare matasa ke tunzara sauran al’umma su je su kada kuri’a a zabe.
An soki salon Gwamnonin Kudu
Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya yi kaca-kaca da taron dangin da ‘Yan Kudu suke yi. Shekarau yace babu dalilin a rika yin barazana kan 2023.
Shekarau yace ya kamata wanda zai gaji Muhammadu Buhari ya fito daga Kudancin Najeriya, amma salon da gwamnonin Kudu suka dauka sam ba daidai ba ne.
Asali: Legit.ng