2023: Saraki ya shirya fafatawa da Atiku yayin da Kawu Baraje yace PDP za ta mika tikiti zuwa Arewa

2023: Saraki ya shirya fafatawa da Atiku yayin da Kawu Baraje yace PDP za ta mika tikiti zuwa Arewa

  • Kawu Baraje, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, ya yi karin haske cewa PDP za ta mika takarar shugaban kasarta zuwa arewa
  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Iyorchia Ayu, a ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba, ya bayyana a matsayin dan takarar PDP a matakin shugabancin jam’iyyar
  • Bayan tantancewar da taron masu ruwa da tsaki na yanki, ‘yan takara uku sun bayyana kafin aka zabi Ayu

FCT, Abuja - Duk da bayyanar tsohon shugaban majalisar dattawa, Iyorchia Ayu a matsayin dan takarar kujerar shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) gabannin babban taronta, Kawu Baraje ya bayyana cewa an amince wa arewa ta shiga takarar shugaban kasa na 2023.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Baraje, wanda ya kasance tsohon shugaban PDP na kasa, ya ce jam’iyyar ta ba arewa damar samar da dan takarar shugaban kasarta a 2023 duk da bayyanar dan arewa, Sanata Iyorchia Ayu.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Jerin manyan jiga-jigan PDP da ke son a bude tikitin jam’iyyar ga dukkan yankuna

2023: Saraki ya shirya fafatawa da Atiku yayin da Kawu Baraje yace PDP za ta mika tikiti zuwa Arewa
2023: Saraki ya shirya fafatawa da Atiku yayin da Kawu Baraje yace PDP za ta mika tikiti zuwa Arewa Hoto: Thde Guardian
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa Baraje ya tabbatar da hakan ne a yayin wata hira da jaridar a ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba.

A bisa ga al’adarta, PDP ta kan mika shugabancinta da kujerar shugaban kasa ga yankuna daban-daban, amma yayin da ta mika kujerar shugabancinta a wannan karon, ta ki mika kujerar shugaban kasa ga kowani yanki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Baraje, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, ya ce arewa ta tsakiya ta so shugabancin kasar ne ba shugabancin jam’iyyar na kasa ba.

Ya ce a matakin da yankin ya samu shugabancin jam’iyyar, toh kada hakan ya hana sa takarar shugaban kasa.

Da yake magana a ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba, kan ko an magance wannan lamari kafin a zabi Ayu ta hanyar bai daya, Baraje ya ce baya daga cikin tanadin a lokacin da suka yanke shawarar zabar Ayu.

Kara karanta wannan

Tsohon Kakakin majalisar dokoki da wasu jiga-jigai sun fice daga jam'iyyar APC, Zasu koma PDP

Ya ce:

“Jam’iyyar ta amince da mu. Ba wai kawai mun yarda da gaskiyar cewa shugaban jam’iyyar zai fito daga arewa ta tsakiya bane, hakan ba zai hana yankin takarar tikitin shugaban kasa ba. Wannan yarjejeniya ce a rubuce.
“Ayu zai iya jagorantar jam’iyyar zuwa ga matakin nasara. Ya kasance Shugaban majalisar dattawa. Ya yi minista. Ya kasance uba ga jam’iyyar. Ya san wa zai tuntuba sannan ya san jagorantar jam’iyya yana bukatar hadin kai ne. Zai zo da duk wadannan gogewar ne. Da yarjejeniyar, An bude tikitin shugabancin kasar ga arewa da kudu.”

Sanatocin PDP sun bada shawarar da za ta faranta ‘Yan siyasan Arewa da Kudu a 2023

A wani labarin, mun kawo a baya cewa Sanatocin jam’iyyar PDP mai hamayya sun kawo shawarar a bar kofar neman takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023 a PDP a bude.

Vanguard ta kawo rahoto cewa wasu Sanatoci sun kawo maganar ayi watsi da tsarin ware wa wani yanki mukami, a bar wanda ya iya allonsa, ya wanke.

Kara karanta wannan

Hotunan Osinbajo na gudu a filin motsa jiki yayin karbar bakuncin gasar Baton

Har yanzu ba a tsaida matsaya a kan wannan batu ba, amma majiyar tace ‘yan majalisar sun bijiro da maganar da nufin a tunkari jam’iyyar APC a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng