Sanatocin PDP sun bada shawarar da za ta faranta ‘Yan siyasan Arewa da Kudu a 2023

Sanatocin PDP sun bada shawarar da za ta faranta ‘Yan siyasan Arewa da Kudu a 2023

  • Sanatocin PDP suna so a bar kofar neman takarar Shugaban kasa a bude
  • Ana tunani jam’iyyar za ta kai tikitin shugaban kasa zuwa Arewa a 2023
  • ‘Yan majalisa sun bijiro da shawara cewa PDP ta kyale kowa ya nemi tuta

FCT, Abuja - Sanatocin jam’iyyar PDP mai hamayya sun kawo shawarar a bar kofar neman takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023 a PDP a bude.

Vanguard ta kawo rahoto cewa wasu Sanatoci sun kawo maganar ayi watsi da tsarin ware wa wani yanki mukami, a bar wanda ya iya allonsa, ya wanke.

Har yanzu ba a tsaida matsaya a kan wannan batu ba, amma majiyar tace ‘yan majalisar sun bijiro da maganar da nufin a tunkari jam’iyyar APC a 2023.

Jaridar tace idan kan Sanatocin ya hadu a kan wannan, za a kai wa gwamnonin jihohi wannan shawara. Daga nan ne maganar za ta iya zuwa gaban NEC.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Wanda ya iya allonsa, ya wanke

“A matsayinmu na Sanatocin PDP, muna duba yiwuwar barin neman kujerar shugaban kasa a zaben 2023 a bude.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanatocin PDP
Wasu Sanatoci a zaman majalisa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“A bar neman tikitin ga kowa, ba tare da an ware wa wani yanki kujerar ba, domin a iya fito da ‘dan takara mai nagarta."
“Kamar yadda kuka sani, za muyi magana da gwamnoninmu, ta yadda za mu zama hau shafi daya. Ba mu amince ba tukuna.”

Majiyar tace har yanzu Sanatocin su na yawo da wannan shawara ne a zauren majalisar tarayya.

NEC ce Majalisar koli a jam’iyya, ita ce za ta zauna ta yanke shawara a kan yadda za a shirya zaben shugabanni, idan kotu ba ta dakatar da gangamin ba.

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, da aka sauke ya shigar da kara, yana kalubalantar cire shi da aka yi kafin karshen wa’adinsa.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Osinbajo zai yi takara?

A farkon makon nan aka ji cewa hotuna sun cika gari, masoya suna yi wa Yemi Osinbajo kamfe tun a yanzu. Jama’a sun wayi gari sun ga fastoci a jihar Osun.

Shugaban kungiyar magoya-baya ta 'Osinbajo for All Volunteer Group', Mr. Peter Ogundeji, yace sune suka cika ko ina da fastocin mataimakin shugaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel