Gabannin zaben 2023, jigon jam’iyyar PDP ya bayyana bukatun Arewa ta tsakiya

Gabannin zaben 2023, jigon jam’iyyar PDP ya bayyana bukatun Arewa ta tsakiya

  • An yi kira ga shugabancin Jam’iyyar PDP da su kasance masu adalci da ba dukkan mambobin jam’iyyar fili su fafata gabanin zaben 2023
  • Alhaji Kawu Baraje ne ya yi wannan kira inda ya ce ya kamata yankin arewa ta tsakiya ya fito da dan takarar shugaban kasa na PDP
  • Baraje ya ce kwararrun 'yan takara daga arewa ta tsakiya za su tsaya kan sanarwar da kwamitin zartarwa na PDP ya yi a baya

FCT, Abuja - Biyo bayan yanke shawarar da Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta yi game da yankin da za ta baiwa kujerar shugabancinta na kasa, tsohon shugaban jam’iyyar, Kawu Baraje, ya ce mambobi daga arewa za su yi takarar neman tikitin shugaban kasa na 2023.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Bareje a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 12 ga watan Oktoba, ya ce kwararrun 'yan PDP daga arewa ta tsakiya za su yi takarar tikitin shugaban kasa a lokacin zaben fidda gwani na jam'iyyar.

Read also

Wata Sabuwa: Matan jam'iyyar PDP Sun bukaci a basu kujerar mataimakin shugaba

Gabannin zaben 2023, jigon jam’iyyar PDP ya bayyana bukatun Arewa ta tsakiya
Gabannin zaben 2023, jigon jam’iyyar PDP ya bayyana bukatun Arewa ta tsakiya Hoto: Abdul Abdul
Source: Facebook

Baraje ya ce arewa ta tsakiya za ta bi sanarwar farko da Kwamitin Zartarwa na Jam’iyyar ta yi wanda hakan ke nuna cewa karkatar da ofisoshin ba zai shafi shawarar mambobi na neman takarar zabe ba.

Tarihin zababbun mukamai na PDP

A cewar Baraje, yankin na son samar da shugaban Najeriya na gaba bayan da ya samar da shugabannin jam’iyyar na ƙasa guda biyar a shekaru 23 na tarihin PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daidaito da adalci ga kwararrun 'yan takarar shugaban kasa da suka cancanta daga arewa ta tsakiya

Jaridar The Cable ta kuma ruwaito cewa tsohon shugaban jam'iyyar na PDP na kasa ya ce yakamata a bar arewa ta samar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar cikin adalci da daidaito.

Ya ce sun kuma lura cewa wasu shugabanni a wajen shiyyar arewa ta tsakiya suna aiki tukuru don tura kujerar shugaban jam’iyyar na kasa zuwa shiyyar don su yi asara.

Read also

Shugabancin 2023: Jerin manyan jiga-jigan PDP da ke son a bude tikitin jam’iyyar ga dukkan yankuna

Dole PDP ta mika shugabancin kasa na 2023 ga yankin Kudu maso gabas, in ji Ikpeazu

A baya mun ji cewa, Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba, ya ce yana da muhimmanci ga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta mika tikitinta na takarar shugaban kasa na 2023 zuwa yankin kudu maso gabashin kasar.

PM News ta ruwaito cewa gwamnan yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar Abia, ya ce kudu maso gabas bata samar da shugaban kasa ba a Najeriya.

Ya ce ya kamata a mikawa kudu maso gabas tikitin takarar shugaban kasa na 2023 ba tare da bata lokaci ba saboda an dade ana mayar da yankin saniyar ware.

Source: Legit.ng

Online view pixel