Babbar Magana: Kotu ta tsige shugaban jam'iyyar APC kan ya saɓa lokaci

Babbar Magana: Kotu ta tsige shugaban jam'iyyar APC kan ya saɓa lokaci

  • Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a birnin Abuja ta tsige Tochukwu Okorie daga matsayin shugaban PDP a jihar Ebonyi
  • Alƙalin Kotun ya kafa hujja da cewa Okorie bai maida Fam ɗin takara a lokacin da PDP ta ɗibar masa ba, dan haka bai cancanta ya shiga zaɓe ba
  • Kotun ta kuma bai wa jam'iyya umarnin ta ba wanda ya zo na biyu takardar shedan zama zaɓaɓɓen shugaba

Ebonyi - Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta tsige Tochukwu Okorie daga matsayinsa na shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Ebonyi.

Da yake yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar gaban Kotun, mai shari'a Ahmed Muhammed, ya ce Okorie ya saɓa wa dokar shiga zaɓe kasancewar ya maida Fam ɗin takara a makare.

Jaridar the Cable ta rahoto cewa Mista Okorie ya maida Fam ɗin sha'awar takara a ranar 4 ga watan Oktoba, 2021, kwanaki kaɗan bayan rufe karɓa a ranar 1 ga Oktoba.

Kara karanta wannan

Wani Gwamnan APC ya gana da Buhari, ya faɗa masa aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa a 2023

Shugaban PDP da aka tsige, Tochukwu Okorie.
Babbar Magana: Kotu ta tsige shugaban jam'iyyar APC kan ya saɓa lokaci Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Okorie ya samu kuri'u 1,240 waɗan da suka dora shi a kan abokin takararsa Silas Onu, tsohon kakakin jam'iyya, wanda ya samu kuri'u 260 a zaɓen da ya gudana ranar 16 ga watan Oktoba.

Bisa rashin gamsuwa da sakamakon, Mista Onu, ya shigar da ƙara yana mai kalubalantar matakan da aka bi, ya jera PDP da Okorie a matsayin na farko na na biyun waɗan da yake ƙara.

Onu ya roki Kotu da ta duba cewa ko Okorie ya cika sharuddan shiga zaɓe ko akasin haka bayan gaza maida Fam a kan lokaci ba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Wane hukunci Kotu ta yanke?

Da yake yanke hukunci, Mai Shari'a Muhammed, ya ce bai kamata Okorie ya ci bulus ba kan abun da ya yi da ya saɓa wa lokaci.

Kara karanta wannan

Idan ban gyara Najeriya a shekara ɗaya ba ku mun kiranye, Ɗan takarar shugaban ƙasa ya roki dama a 2023

Ya ce:

"A ra'ayin wannan Kotu, wanda ake ƙara na biyu ya ƙauracewa maida Fam ɗin nuna sha'awar takara a jadawalin lokacin da jam'iyyar PDP ta ware."
"Duk da abun da ya yi, an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓe, bai kamata a bar shi ya amfana da kuskuren da ya yi.

Daga nan, Alkalin ya umarci jam'iyyar ta baiwa Mista Onu shaidar zama zaɓaɓɓe, inda ta ayyana shi a matsayin halastaccen shugaban APC a Ebonyi.

A wani labarin kuma Bayan Sanata Adamu, wani babban Jigon APC ya yi murabus daga kujerarsa

Donald Ojogo, ya miƙa takardar murabus ɗinsa daga gwamnatin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ba tare da jinkiri ba.

Gwamna Akeredolu, idan ba ku manta ba ya ba hadimansa dake niyyar takarar siyasa awanni 48 su aje muƙamansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262