Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya yi magana rikicin shugabancin APC da ranar babban taro

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya yi magana rikicin shugabancin APC da ranar babban taro

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gargaɗi mambobin APC kowa ya koma cikin hankalisa yayin da babban taro ke karatowa
  • Buhari ya bukaci jagororin jam'iyya su dakatar da kiran suna da kuma sukar junansu a kafafen watsa labarai
  • Shugaban ƙasan ya kuma jaddada cewa babban taron APC na ƙasa na nan daram ranar 26 ga watan Maris

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi tsokaci kan rikicin shugabanci da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

A wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar a Facebook, shugaba Buhari ya gargaɗi jagororin APC da su guji kiran suna da cin dudduniyar junansu.

Shugaban ƙasa ya kuma jaddada cewa babban ganganmin jam'iyyar APC na ƙasa na nan daram ranar da aka tsara 26 ga watan Maris 2022.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An kuma sace kananan yara yan shekara 4 a Keke Napep bayan tashi daga makaranta

Shugaba Muhammadu Buhari
Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya yi magana rikicin shugabancin APC da ranar babban taro Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Haka nan Buhari ya roki mambobin APC da su kawar da duk wani saɓani dake tsakanin su, kuma su haɗa kai matukar suna son jam'iyyar ta cigaba da samun nasara a dukkan matakai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A sanarwan an jiyo shugaba Buhari na kira ga mambobin APC kan, "Su duba babbar jam'iyyar hamayya PDP yadda ta koyi darasi daga rashin haɗin kai, rashin jagoranci da cin hanci."

Buhari ya ce:

"Sun gaza a tsawon shekara 16 a kan gadon mulki kuma sun gaza a tsagin hamayya. Eh mu ma a APC muna da namu matsalolin cikin gida, abu ne da ya saba faruwa a kowace jam'iyya."
"Yayin da ƙasa ke shirin zaben shugaban ƙasa a 2023, ba bukatar cece-kuce da saɓani kan wasu lamurra, ba faɗa da juna ya kamata mu yi ba a yanzu. Wajibi a jingile duk wasu matsaloli kafin babban taro."

Kara karanta wannan

Shugaban PDP ya yi magana kan gwamnan dake shirin ficewa ya koma jam'iyyar APC

Jam'iyyar APC ta fara da sa'a - Buhari

Shugaban ya kuma bugi ƙirjin cewa jam'iyyar APC ta taki babban nasara tun farkon zuwanta kuma ta samu kwarin guiwar nasara a kashi biyu cikin uku na jihohin Najeriya.

"Wannan jam'iyya ta kafu na tsawon shekara Takwas, ta zama gagara ba dau domin ta buɗe wa kowa ƙofar shiga a dama da shi, babba da ƙarami."
"Kari akan haka shi ne ba mu fara da jin karfin mulki ba, ko ganin muna da gwamnati, mun haɗa kan mu tun farko domin kawo cigaba ba tare da nuna banbancin addini, siyasa ko yare ba."

A wani labarin kuma gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya yi ikirarin cewa har yanzun yan Najeriya ba su da zaɓin da ya fi APC

Malam Nasiru El-Rufa'i ya ce duk da mutane sun tsammaci abin da ya fi haka, amma idan aka kwatanta ba kamar APC.

Haka nan kuma gwamnan ya ce ba ya sha'awar neman wata kujerar siyasa a shekarar 2023, bayan kammala mulkin Kaduna yana son hutu.

Kara karanta wannan

Tsige Mala Buni: Gwamnoni 2 da Minista sun garzaya Landan, za su sa labule da Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262